Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a yau Laraba ta gurfanar da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Alhaji Yakubu Adamu, da wasu mutane uku a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kan zargin tallafa wa ta’addanci.
Mutane ukun da aka gurfanar ɗin su ne Balarabe Abdullahi Ilelah, Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed.
An gurfanar da su ne kan tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi haɗin baki, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma zargin tallafa wa ta’addanci, wanda ya saɓa wa Sashe na 2(1) da Sashe na 19(1)(d), kuma abin hukunci ne ƙarƙashin Sashe na 19(2)(b) na Dokar Hana da Ƙwace Kuɗaɗen Haramtattu (Money Laundering (Prevention and Prohibition) Act), 2022.
Lauyan masu gabatar da ƙara, Samuel Chime, ya shaida wa kotu cewa an kawo shari’ar ne domin gurfanarwa, yana roƙon a karanta tuhumar ga waɗanda ake ƙara.
“Mun shigar da tuhume-tuhume guda goma, masu kwanan wata 30 ga Disamba, 2025, kuma a ranar aka shigar da su,” inji shi.
Ɗaya daga cikin tuhumar ta ce: “Kai Yakubu Adamu (a matsayin ka na Kwamishinan Kuɗi na Gwamnatin Jihar Bauchi), a wani lokaci cikin shekarar 2024, a cikin hurumin wannan kotu mai daraja, ka karɓi kuɗi a hannu har dalar Amurka miliyan shida da dubu ɗari tara da hamsin (USD 6,950,000), ba ta hanyar wata cibiyar kuɗi ba; hakan ya saɓa wa Sashe na 2(1) da Sashe na 19(1)(d), kuma abin hukunci ne ƙarƙashin Sashe na 19(2)(b) na Dokar Hana da Ƙwace Kuɗaɗe Haramtattu, 2022.”
Wata tuhuma kuma ta ce: “Kai Yakubu Adamu (a matsayin ka na Kwamishinan Kuɗi na Gwamnatin Jihar Bauchi), Sirajo Jaja (Babban Akanta na Jihar Bauchi, yanzu ya ɓuya daga shari’a), Samaila Irmiya Liman (shi ma ya ɓuya daga shari’a), Balarabe Abdullahi Illelah, Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed (duk ma’aikatan gwamnati ne kuma masu sanya hannu kan asusun gwamnati da/ko takardun biyan kuɗi na Jihar Bauchi), a tsakanin watan Janairu 2024 zuwa Mayu 2024, a cikin hurumin wannan kotu mai daraja, kun haɗa baki wajen bayar da kuɗi a hannu jimillar kusan dalar Amurka miliyan biyu da dubu ɗari uku (USD 2,300,000) domin amfanin Bello Boɗejo da mutanen da ke da alaƙa da shi, bisa amincewar da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed, ya bayar, tare da dalilai masu ma’ana na yarda cewa za a yi amfani da waɗannan kuɗaɗen, gaba ɗaya ko wani ɓangare, wajen tallafa wa ɗan ta’adda ko ƙungiyar ta’addanci; hakan ya saɓa wa Sashe na 26(1) kuma abin hukunci ne ƙarƙashin Sashe na 21(2)(a) na Dokar Hana da Ƙwace Ta’addanci (Terrorism (Prevention and Prohibition) Act), 2022.”

Waɗanda ake zargin dai sun musanta laifin da aka karanta masu, inda suka ce “ba mu aikata ba,” lamarin da ya sa lauyan gwamnati, Samuel Chime, ya nemi kotu ta sanya ranar fara shari’a.
“Za mu nemi rana domin mu buɗe shari’ar,” inji Chime.
A nasa martanin, lauyan waɗanda ake ƙara ya shaida wa kotu cewa ɓangaren tsaro ya shigar da buƙatun beli daban-daban a madadin waɗanda ake ƙara.
“Mun shigar da buƙatun beli daban-daban ga wanda ake ƙara na farko, na biyu, na uku da na huɗu, kuma duka an shigar da su ne a ranar 30 ga Disamba, 2025,” inji shi.
A martanin sa, Chime ya ce ɓangaren gwamnati an yi masu hidimar takardun, kuma sun riga sun shigar da takardar ƙin amincewa ta haɗin gwiwa.
“An yi mana hidima, mun shigar da takardar ƙin amincewa ta haɗin gwiwa jiya, ran ka ya daɗe, 30 ga Disamba, 2025,” inji shi.
Mai Shari’a Emeka Nwite daga bisani ya ɗage shari’ar domin yanke hukunci kan buƙatar beli zuwa ranar 5 ga Janairu, 2026, tare da umurnin tsare waɗanda ake ƙara a Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT).







