’Yan sanda sun kama mutane takwas da ake zargi da aikata garkuwa da mutane bayan wani samame na tsaro na haɗin gwiwa da aka gudanar a ƙauyen Rukubi da ke Ƙaramar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa.
Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, DCP Anthony Okon Placid, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai a wannan Juma’a cewa an gudanar da aikin ne bayan samun rahoton gaggawa a safiyar yau, 7 ga Mayu, 2026, dangane da wani hari da wasu ’yan bindiga suka kai bayan sun mamaye ƙauyen a daren jiya, suna ta harbe-harbe barkatai tare da haddasa firgici a tsakanin mazauna yankin.
Ya ce: “A yayin harin, an ruwaito cewa maharan sun kutsa cikin gidajen wasu mazauna biyu tare da yin garkuwa da mutum biyu zuwa wani wuri da ba a sani ba.
“Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda na Rundunar Jihar Nasarawa, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da matasan al’umma na yankin, sun gaggauta isa wurin tare da ƙaddamar da samamen haɗin gwiwa wanda ya kai ga kama mutum takwas da aka alaƙanta da lamarin.”

Waɗanda aka kama sun haɗa da Adamu Alfa, Muhammed Alfa, Shu’aibu Alfa, Usman Alfa, Ali Alfa, Isa Alfa, Adamu Alfa, da Ja’afaru Alfa, dukkan su daga Rugan Alhaji Alfa da ke ƙauyen Rukubi.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ƙara da cewa a yayin aikin, jami’an tsaro sun ƙwato bindigogi biyu ƙirar AK-47, babura huɗu ƙirar Bajaj, da kwanson harsasai biyu na 7.62mm da aka harba, waɗanda ake zargi da harin.
A cewar sa, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya samu munanan raunuka a yayin artabun, kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwar sa yayin da yake karɓar magani.
Ya ce: “Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, psc(+), NPM, ya yaba da jarumtaka da ƙwarewar jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai bayyana nasarar a matsayin wata babbar shaida ta ingancin aikin ’yan sanda da ke amfani da bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar hukumomi wajen yaƙi da manyan laifuffuka masu tada hankali.
“Haka kuma ya yaba da gagarumar gudunmawar hukumomin tsaro na abokan aiki, ƙungiyoyin sa-kai na tsaro, matasan al’umma, da mazauna yankin, waɗanda haɗin kan su ya taimaka matuƙa wajen samun wannan nasara.”







