• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
April 25, 2026
in Tsaro
A A
0
Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

Rundunar sojin Nijeriya a yau Juma’a ta ƙaddamar da Babbar Kotun Soja domin gurfanar da jami’an da ake zargi da kitsa juyin mulki, lamarin da ya nuna fara shari’ar a hukumance.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an kawo jami’an da ake tuhuma wurin zaman kotun, wato Guards Brigade Scorpion Mess da ke Asokoro, da misalin ƙarfe 8:53 na safe ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

Sai dai an hana ‘yan jarida shiga cikin ɗakin kotun yayin da aka fara shari’ar a rufe.

An kuma ga wasu lauyoyi masu zaman kan su sun isa wurin tun kafin ƙaddamar da kotun, abin da ke nuna akwai wakilan shari’a na waɗanda ake tuhuma.

Zaman kotun ya nuna fara tsarin shari’ar cikin gida na rundunar soji bayan watanni ana gudanar da bincike kan wannan zargin makircin juyin mulki.

Lamarin ya samo asali tun a watan Oktoban 2025 lokacin da aka kama kimanin jami’an soja 16 masu aiki, ciki har da manya da ƙanana, bisa zargin aikata laifukan rashin ɗa’a a aikin soja.

Sai dai binciken da hukumomin soji suka yi daga baya ya tabbatar da cewa wasu daga cikin jami’an suna da tambayoyin da za su amsa dangane da zargin yunƙurin kifar da gwamnatin da kundin tsarin mulki ya assasa, lamarin da ya kai ga yanke shawarar gurfanar da su a gaban kotun soja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa an kawo fiye da jami’ai 30 da ake tuhuma cikin wata motar safa ƙirar Marco Polo.

A wani labarin mai nasaba da wannan, tun da farko Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da wasu fararen hula da tsofaffin jami’an soja a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan wannan zargin juyin mulki.

Waɗanda ake tuhuma, ciki har da wani ritaya Manjo Janar da kuma jami’in ‘yan sanda mai aiki, an tuhume su da laifuka masu nasaba da cin amanar ƙasa da ta’addanci.

Dukkan su sun musanta zarge-zargen da ake musu.

Daga bisani kotun ta bayar da umurnin ci gaba da tsare su har sai an saurari buƙatun su na beli.

Gudanar da waɗannan shari’o’i a layi biyu na nuna tsarin da ake bi, inda jami’an soja masu aiki ke fuskantar kotun soja, yayin da fararen hula da tsofaffin jami’an soja ke fuskantar shari’a a kotunan farar hula.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani kan yadda shari’ar kotun sojan ke gudana ba.

Tags: juyin mulkikotushari'asoja
Previous Post

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

Next Post

A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!