Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, a yau Laraba ya fice daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) wadda ke samun goyon bayan haɗakar jam’iyyu.
Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya bada sanarwar wannan mataki ne a ranar Talata yayin wani taro da aka gudanar a otal ɗin Nike Lake Resort da ke Inugu.
“Mun kammala wannan shekara ne da fatan cewa a shekarar 2026 za mu fara tafiyar ceto,” inji Obi.
“Za mu yi tir da mabuɗin zaɓe ta kowace hanya ta doka a shekarar 2027.
“Har yanzu muna da wa’adin shekara guda ga kowa da kowa ya je ya tabbatar da makarantun da ya halarta.
“Ba ma son mu koma kotu kuma daga baya a ce mana batun kafin zaɓe ne.
“Tsarin kafin zaɓe ya kamata ya fara tun yanzu.”
Shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, yana daga cikin waɗanda suka halarci taron.
Haka kuma akwai tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal; da tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai,Emeka Ihedioha, Sanata Ben Obi; Sanata Victor Umeh; Sanata Tony Nwoye; Sanata Gilbert Nnaji; Sanata Enyinnya Abaribe; Sanata Sam Egwu; Onyema Ugochukwu, tare da sauran ‘yan majalisa da manyan baƙi.
Obi dai ya yi murabus daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar 25 ga Mayu, 2022, yana mai cewa “sababbin abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar ba sa goyon bayan gudunmawa mai ma’ana”.
Daga nan ya shiga jam’iyyar LP a ranar 27 ga Mayu, 2022, kuma ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar — inda ya zo na uku.







