• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

ALI KANO by ALI KANO
May 13, 2026
in Tsaro
A A
0
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Jami’an kamfanin MARSS UK Ltd da abokin hulɗar su na Nijeriya, MPS Mikopowers Ltd, suna nuna tsarin tsaro da na tattara bayanan sirri ga Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), da tawagar sa yayin ziyarar aiki da suka kai ƙasar Monako kwanan nan.

Jami’an kamfanin MARSS UK Ltd da abokin hulɗar su na Nijeriya, MPS Mikopowers Ltd, suna nuna tsarin tsaro da na tattara bayanan sirri ga Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), da tawagar sa yayin ziyarar aiki da suka kai ƙasar Monako kwanan nan.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya sake jaddada aniyar Nijeriya ta sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwar dabaru, bunƙasa ƙwarewar cikin gida, musayar fasaha, da ɗorewar haɗin gwiwar masana’antar tsaro.

Ministan ya bayyana haka kwanan nan yayin ziyarar aiki da ya kai ƙasar Monako tare da manyan jami’an ma’aikatar.

Ya yi wannan bayani ne dangane da aiwatar da shirin da aka gabatar na “Multi-domain Hybrid Intelligence Shield” (HIS) ga Ma’aikatar Tsaro, wanda shi da tawagar sa suke tattaunawa a kai da kamfanin MARSS UK Ltd da abokin hulɗar su na Nijeriya, MPS Mikopowers Ltd.

Tawagar ta samu tarba daga jami’an MARSS UK Ltd da MPS Mikopowers Ltd, waɗanda suka gabatar da cikakkun bayanai tare da nuna yadda tsarin NiDAR na haɗaɗɗen umurni da sarrafawa ke aiki kai-tsaye, da fasahohin yaƙi da jiragen sama marasa matuƙa (drone), dandamalin sa ido na tafi-da-gidan-ka, da hanyoyin tsaron iyakoki da aka tsara domin ƙarfafa ƙarfin tsaro da kariyar Nijeriya.

Ziyarar ta mayar da hankali ne kan gwaje-gwajen aiki kai-tsaye, tattaunawar fasaha, da shawarwari na dabaru da ke da nufin inganta tsarin tsaron ƙasa na Nijeriya ta hanyar ingantattun fasahohin umurni, sarrafawa, sa ido, da haɗaɗɗun hanyoyin tsaro.

Musa ya jaddada muhimmancin gina ƙwarewar aiki ta cikin gida yayin da ake cin gajiyar ƙwarewar ƙasashen waje domin tunkarar sabbin barazanar tsaro, ciki har da ta’addanci, rashin tsaron iyakoki, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, fashin teku, da kuma ƙarin barazanar da jiragen sama marasa matuƙa ke haifarwa.

Ya tuna cewa ma’aikatar ita ce cibiyar tsara dabarun tsarin tsaron ƙasar.

Ya ce: “Saboda haka dole ne mu yi amfani da fasaha wajen tattara bayanan sirri, sa ido, da ayyukan sabis na ci gaba. Muna da abokan hulɗa da ƙawayen da ke shirye su tallafa mana. Za mu tuntuɓe su domin mu yi aiki tare a matsayin ƙungiya.”

Yayin tattaunawar, tawagar Nijeriya ta kalli gwaje-gwajen aiki kai tsaye na tsarin gano abubuwa ta radar, tantance barazana da basirar wucin gadi (AI) ke taimakawa, damar daƙile jiragen sama marasa matuƙa, da hanyoyin haɗaɗɗen tsarin umurni da sarrafawa na ƙasa.

Tattaunawar ta kuma shafi shirin kafa cibiyoyin umarni na ƙasa da na yankuna, rundunonin mayar da martani masu tafi-da-gidan-ka, da kuma Cibiyar Ƙwarewa ta Musamman domin kwaikwayon atisaye, horo, da bunƙasa manufofin aiki.

Mataimakiyar Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Tsaro, Enderline Chukwu, ta ce a cikin wata sanarwar manema labarai: “Ziyarar ta ba da dama don tattaunawa kan haɗin gwiwar masana’antar tsaro, tallafa wa samar da kayayyaki a cikin gida, haɗa fasaha, da shirye-shiryen haɗin gwiwa na dogon lokaci tsakanin cibiyoyin tsaron Nijeriya da masu ruwa da tsaki na ƙasa da ƙasa.

“Ana sa ran wannan hulɗa za ta ƙara ƙarfafa ƙoƙarin Nijeriya na inganta tsaron ƙasa, bunƙasa haɗin kai tsakanin hukumomi, da ciyar da manufofin sabunta tsaron ƙasar gaba.

“Wannan ziyarar aiki wani ɓangare ne na faɗaɗa diflomasiyyar tsaro da shirye-shiryen hulɗar dabaru na Nijeriya da ke nufin inganta zaman lafiyar yankin, ingancin ayyuka, da juriyar ƙasa a cikin yanayin tsaro na duniya mai sauyawa.”

Tags: Christopher MusadabaruMonacotsaro
Previous Post

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

Next Post

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!