• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙara ƙarfi a watan Disamba, yayin da malejin hadahadar kamfanoni da masana’antu ya kai maki 57.6 – CBN

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
January 1, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya tashi haiƙan: Malejin farashin kayayyaki ya ƙara yin ƙasa zuwa kashi 16.05, yayin da asusun kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 46.7
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa saɓatta-juyattar ayyukan tattalin arzikin cikin gida sun ci gaba da ƙarfafa a watan Disamba 2025, yayin da malejin ƙarfin hadahadar masana’antu, wato ‘Composite Purchasing Managers’ Index’ (PMI) ya ci gaba da kasancewa sama da maki 50. Hakan dai kenan ya nuna irin yadda ake samun faɗaɗar ayyukan tattalin arziki.

Rahoton binciken PMI na watan Disamba 2025 da Babban Bankin ya fitar ya nuna cewa ƙarfin PMI ya kai maki 57.6, wanda ke tabbatar da samun bunƙasar tattalin arziki mafi ƙarfi da aka samu a kusan shekaru biyar da suka gabata.

Rahoton ya ce wannan ci gaba mai ɗorewa ya samo asali ne daga faɗaɗa ayyuka a manyan sassa da ke samar da ayyukan yi.

“Sakamakon PMI na ɓangarori ya nuna cewa harkokin noma da ayyukan gona ya ci gaba da ƙarfi da maki 58.5, masana’antu sun samu maki 57.0, yayin da ɓangaren ayyukan yau da kullum ya kasance a yanayi mai kyau da maki 51.9.

“Wannan yana nuna ci gaba mai yawa a ɓangaren kayan da ake fitarwa da ayyukan kasuwanci a cikin watan,” inji rahoton.

Binciken ya kuma nuna cewa sassa 32 daga cikin 36 da ake sa-ido a kan su sun samu ƙaruwa kamar a matakan sabbin odar kasuwanci da ayyukan yi.

A cewar wata sanarwa daga Hakama Sidi-Ali, Daraktar Rijo ta Sashen Sadarwa na Kamfanoni a CBN, ta ce wannan sakamako yana nuna dawowar buƙatar kayayyakin cikin gida a hankali da ƙarfafa ayyukan samarwa, musamman a ɓangaren tattalin arziƙin da ba na mai ba.

“Bankin ya danganta ƙarin ingantuwar PMI da tasirin kyawawan matakan da ake ɗauka na daidaita tattalin arziƙi, ciki har da ƙoƙarin inganta yanayin aiki da tsare-tsaren da ke gamsar da ’yan kasuwa tare da yin amanna da tsarin da ake a kai.

“Waɗannan gyare-gyaren sun ci gaba da ƙarfafa samar da ayyukan yi da kuma kyakkyawan fata game da makomar tattalin arziki a zangon ƙarshe na shekarar 2025,” inji ta.

Hakama ta ƙara da cewa bayanan PMI na watan Disamba ya ƙarfafa tsammanin tabbataccen yanayin ci gaban tattalin arziki yayin da Nijeriya ke shiga sabuwar shekara.

Tags: CBNHakama Sidi Alitattalin arziki
Previous Post

Zargin tallafa wa ta’addanci: EFCC ta gurfanar da kwamishinan Bauchi da wasu 3 kan $9.7m

Next Post

Za mu zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin murƙushe barazanar tsaro a 2026 – Tinubu

Related Posts

Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Nagartattun sauye-sauyen CBN kan manufofin tattalin arziki sun haddasa ambaliyar masu sha’awar zuba jari daga ƙasashen waje

May 14, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Next Post
Za mu zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin murƙushe barazanar tsaro a 2026 – Tinubu

Za mu zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin murƙushe barazanar tsaro a 2026 - Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!