• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
April 17, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Khalifa Bawa tare da tarin kayan haɗa makamai da sojoji suka samu a motar sa

Khalifa Bawa tare da tarin kayan haɗa makamai da sojoji suka samu a motar sa

Dakarun rundunar Sojojin Nijeriya na Operation Enduring Peace waɗanda aka jibge a garin Manchok a Jihar Kaduna, tare da karin goyon bayan rundunar musamman ta Special Forces Tactical Team, sun cafke wasu ɗimbin alburusai masu nauyi da kuma kayayyakin da ake zargin na haɗa bamabamai ne a yayin wani bincike na musamman da suka gudanar a jihar.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:45 na safe a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026, kusa da Makarantar Sakandare ta Maza da ke kan hanyar Manchok zuwa Jos.

Ya ƙara da cewa wata mota ƙirar Opel Wagon mai launin shuɗi mai duhu, wadda ke ɗauke da lambar rajista NSR 154 TA Kano, na ɗauke da fasinjoji bakwai ne a cikin ta.

Bayan dakatar da motar, dakarun sun gudanar da cikakken bincike wanda ya kai ga gano wani babban tarin albarusai masu haɗari da aka ɓoye a cikin motar.

Kayayyakin da aka samu sun haɗa da harsasai guda 569 na bindigar harbo jirgin sama (Anti-Aircraft, AA) mai girman 12.7mm, da wasu manyan makamai masu saurin gaske, da kuma harsasai guda 189 na bindigar 7.62mm da aka riga aka harba.

Tarin kayan haɗa makamai da sojojin suka kama

Bugu da ƙari, binciken ya kuma bankaɗo wasu tsofaffin wayoyin hannu na GSM, “waɗanda masana fasaha ke yawan bayyana su a matsayin muhimman sassan da ake amfani da su wajen ƙera bamabamai masu fashewa daga nesa.”

A yayin tambayoyin farko a wurin, direban motar, wanda aka bayyana sunan sa a matsayin Malam Khalifa Bawa, ya yi ƙoƙarin nesanta kan sa da kayan, inda ya ce kayan suna cikin kaya ne da aka tura (waybill).

Bawa ya yi iƙirarin cewa wani mutum da ba a san ko wanene ba shi ne ya ba shi kayan, kuma ya ce ba shi da wata hanyar tuntuɓar ko bayanin wanda ya aiko da kayan ko wanda za a kai wa.

Bawa ya yi iƙirarin cewa wani mutum da ba a san ko wanene ba shi ne ya ba shi kayan, kuma ya ce ba shi da wata hanyar tuntuɓar ko bayanin wanda ya aiko da kayan ko wanda za a kai wa.

A halin yanzu, dukkan waɗanda ke cikin motar, ciki har da wanda ake zargi, tare da motar da kayayyakin da aka kama, suna tsare “domin gudanar da cikakken bincike na ƙwaƙwaf da kuma zurfafa bincike.”

Oteh ya ce: “Dakarun suna ƙoƙarin gano inda aka samo waɗannan kaya da kuma gano babbar hanyar sadarwar da ke da hannu a ƙoƙarin safarar waɗannan kayan yaƙi daga jiha zuwa jiha.”

Tags: Chinonso Polycarp OtehKhalifa BawamakamaiOperation Enduring Peace
Previous Post

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

Next Post

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Tsaro

April 11, 2026
Next Post
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!