• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Tawagar motocin kwamandan rundunar soji ta daƙile mummunan kwanton ɓauna a Kebbi, ta hallaka ’yan ta’adda 5, ta ƙwace tarin makamai

ALI KANO by ALI KANO
February 23, 2026
in Tsaro
A A
0
Tawagar motocin kwamandan rundunar soji ta daƙile mummunan kwanton ɓauna a Kebbi, ta hallaka ’yan ta’adda 5, ta ƙwace tarin makamai
Gawarwakin 'yan ta'adda a inda sojoji suka yi ba-ta-kashi da su

Gawarwakin 'yan ta'adda a inda sojoji suka yi ba-ta-kashi da su

Tawagar motocin Babban Kwamandan Runduna (GOC) ta 8 kuma Kwamandan Sashi na 2 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta North-west Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Bemgha Koughna, ta daƙile wani kwanton ɓauna da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne suka shirya a kusa da Tudun Mayama a Jihar Kebbi.

Harin ya faru ne yayin da tawagar GOC ɗin take kan hanyar ta ta zuwa duba dakarun da ke kan gaba a jihar.

A wata sanarwar manema labarai da Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soji ta 8, Rundunar Sojin Nijeriya / Sashi na 2 na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya fitar a yau Litinin, ya bayyana cewa tawagar ta fuskanci harbi mai tsanani ba zato ba tsammani daga ’yan ta’adda masu ɗauke da makamai yayin da suke wucewa ta cikin dazuzzukan yankin da ke da haɗari.

Ya ce: “Da nuna ƙwarewa ta musamman wajen jagoranci da dabarun yaƙi, Manjo Janar Koughna da dakarun sa sun mayar da martani da ƙarfi, inda suka hallaka ’yan ta’adda biyar tare da fatattakar kwanton ɓaunar.

“Wannan aiki ba kawai ya kare tawagar ba ne, har ma ya tarwatsa shirye-shiryen ’yan ta’addan, tare da isar da saƙo mai ƙarfi na tsoratarwa ga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da suka daɗe suna addabar al’ummomin yankin.

“Bayan nasarar da aka samu, dakarun sun gudanar da cikakken bincike a yankin, inda suka ƙwato tarin makamai da kayayyakin bayanan sirri masu yawa.”

 

Ya ƙara da cewa kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindiga samfurin OJC guda ɗaya, bindiga PKT guda ɗaya, bindigogi AK-47 guda biyu da kuma kwandunan harsasai na AK-47 guda huɗu.

Sauran sun haɗa da laya (bandolier) guda ɗaya ta harsasan PKT, harsasai da dama na 12.7mm, jakar raƙumi mai ɗauke da kuɗi Naira 840,000, wayoyin hannu guda biyu da babura guda biyar.

Osoba ya ce: “A halin yanzu, dakarun na nan a yankin cikin shiri da taka-tsantsan, suna tabbatar da cikakken iko domin hana sake faruwar hare-hare.

“Wannan aiki ya nuna jajircewar Runduna ta 8 ta Sojin Nijeriya wajen kare fararen hula da kuma kawar da barazanar ta’addanci a yankin Arewa-maso-yamma.”

Tags: JanarBemghaKoughnakwantonbaunaLakurawasojojita'addancitsaro
Previous Post

Yadda Aka Raba Musulmi Da Ƙur’ani

Next Post

El-Rufai ya yi ƙarar ICPC kan binciken da ta yi a gidan sa

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
El-Rufai ya yi ƙarar ICPC kan binciken da ta yi a gidan sa

El-Rufai ya yi ƙarar ICPC kan binciken da ta yi a gidan sa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!