• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Zargin yi wa wayar Ribaɗu kutse: Kotu ta sanya ranar 23 ga Afrilu domin gurfanar da El-Rufai

Fati Abdul by Fati Abdul
February 25, 2026
in Tsaro
A A
0
El-Rufai ya rubuta wa Ribaɗu takardar neman ƙarin haske kan zargin shigo da ‘guba mai haɗari’
Daga hagu: Malam Nuhu Ribaɗu da Malam Nasir El-Rufai

Daga hagu: Malam Nuhu Ribaɗu da Malam Nasir El-Rufai

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, zuwa ranar 23 ga Afrilu domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Hukumar DSS ce ta shigar da tuhume-tuhume guda uku a kan sa kan zargin sa da ido da katsalandan ba bisa ƙa’ida ba a harkokin sadarwa, bayan wasu kalamai da ya yi a wata hira ta talbijin.

Tun da farko dai kotun ta sanya ranar 25 ga Fabrairu domin gurfanar da tsohon gwamnan.

Tsohon gwamnan bai halarci zaman kotun na yau Laraba ba.

Lauyan DSS, Oluwole Aladedoyin, ya sanar da kotun cewa har yanzu tsohon gwamnan yana hannun hukumar ICPC, inda ake ci gaba da binciken sa kan zargin karkatar da kuɗaɗe.

Hakan ya sa mai shari’ar ta dage shari’ar zuwa ranar 23 ga Afrilu domin gurfanar da shi.

A makon da ya gabata, Gwamnatin Tarayya, ta hannun DSS, ta shigar da tuhume-tuhume guda uku kan El-Rufa’i bisa zargin kutse a sadarwar Ribaɗu.

El-Rufa’i ya faɗa a wata hira cewa shi da wasu da bai ambaci sunayen su ba sun saurari tattaunawar wayar Ribaɗu bayan wani ɓangare na uku ya sa mata ido. Duk da amincewar sa cewa irin wannan katsalandan ɗin ya saɓa wa doka, sai ya ce irin sa ido na haramtacciyar hanya ba sabon abu ba ne, domin wai gwamnati ma tana yi.

A cewar takardar tuhuma da gidan Channels ya samu a ranar Litinin, gwamnati ta bayyana cewa El-Rufa’i ya amince cewa shi da abokan hulɗar sa sun yi wa wayar Ribaɗu kutse sun saurari maganar sa.

Tuhumar da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya ta Nijeriya, Sashen Shari’a na Abuja, ta bayyana Gwamnatin Tarayya a matsayin mai ƙara, yayin da El-Rufa’i yake matsayin wanda ake ƙara.

Tags: JoyceAbdulmalikkotukutseNasirElrufaiRibaɗushari'awaya
Previous Post

Taron Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗaɗe: CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa 26.5%

Next Post

Sabon Sufeto-Janar Olatunji Disu ya karɓi ragamar aiki: Shin wanene shi?

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa
Tsaro

’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa

May 8, 2026
Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
Next Post
Sabon Sufeto-Janar Olatunji Disu ya karɓi ragamar aiki: Shin wanene shi?

Sabon Sufeto-Janar Olatunji Disu ya karɓi ragamar aiki: Shin wanene shi?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!