• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Taron Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗaɗe: CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa 26.5%

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
February 24, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Taron Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗaɗe: CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa 26.5%
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso

Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi (MPC) na Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya rage Ƙayyadadden Adadin Kuɗin Ruwa (MPR) daga kashi 27% bisa 100% zuwa 26.5%. bisa 100%.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, shi ne ya sanar da rage kuɗin ruwan a wani taron manema labarai ranar Talata, yayin taron MPC na 304 da aka gudanar a Abuja.

Wannan ragi shi ne mafi ƙanƙanta tun bayan taron watan Mayu 2024, lokacin da kuɗin ruwan ya kasance 26.25%.

MPR shi ne babban ma’aunin geji da adadin kuɗin ruwa a tattalin arziki, domin yawancin sauran kuɗaɗen ruwa a ƙasa ana gina su ne a kan sa.

Dalilan Rage Kuɗin Ruwa

Matakin MPC ya biyo bayan saukar hauhawar farashin kayan masarufi da na amfanin yau da kullum a Nijeriya zuwa 15.1% a Fabrairu 2026.

Haka kuma, wannan na zuwa ne watanni shida bayan da aka rage kuɗin ruwan zuwa 27% a Satumba 2025.

A wajen taron manema labarai, Cardoso ya ce mambobin kwamitin sun amince baki ɗaya da rage kkuɗinruwan da maki 50 daga 27% zuwa 26.5%, yayin da aka bar sauran tsare-tsare gejin adadin manufofin kuɗaɗe ba tare da canji ba.

Sauran Muhimman Tsare-tsare

Gwamnan CBN ya bayyana cewa adadin Tsabar Kuɗi da bankunan kasuwanci za su riƙa ajiyewa, ba tare da sun bayar da su lamuni ba wato ‘Cash Reserve Ratio’ (CRR) zai ci gaba da kasancewa:

45% bisa 100.

Su kuma bankunan ‘marchant’, na su adadin zai kasance kashi 16%.

Haka kuma a wurin taron an amince da kashi 75% matsayin adadin kuɗaɗen da ma’aikatun gwamnati, cibiyoyi da hukumomi za su riƙa ajiyewa a asusun ajiyar kuɗaɗen gwamnati da ba na bai-ɗaya ba, wato non-TSA.

An Amince Da Kashi 30% Matsayin Kuɗin Lukudin

(Liquidity Ratio)

Dukkannin mambobin kwamitin a ta bakin Cardoso, sun bar wannnan geji wajejan +50/-450 na adadin ƙayyadadden kuɗin ruwa.

Kwamitin ya ce an yanke shawarar ne bayan cikakken nazari kan haɗurran tattalin arziki, wanda ke nuna cewa saukar hauhawar farashi na ci gaba.

Cardoso ya ƙara da cewa malejin ƙididdigar saukar farashi saukar a muzanin tsakanin wannan shekara da ta bayan ta, wato shekara-shekara a Janairu 2026, ya zama karo na 11 a jere kenan yana sauka tare da samun raguwa.

Hasashen Gaba

CBN ya bayyana cewa ana sa ran ƙarin saukar hauhawar farashi zai ci gaba, sakamakon wanzuwar darajar canjin kuɗi da kuma ingantuwar wadatar abinci.

Sai dai Cardoso ya yi gargaɗi cewa ƙarin kashe-kashen maƙudan kuɗaɗe musamman masu nasaba da zaɓe mai zuwa na 2027, na iya haifar da hauhawar farashi nan gaba.

Karuwar Ajiyar Kuɗaɗen Waje

CBN ya kuma bayyana cewa gejin adadin ajiyar kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 50.45 zuwa ranar 16 ga Fabrairu 2026. Wannan adadi kuwa shi ne mafi girma cikin shekaru 13.

Kwamitin ya danganta wannan da:

  • Ƙarin kuɗaɗen shiga daga fitar da kaya waje,
  • ƙarin kuɗaɗen turo kuɗi daga ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, wato remittance
  • da kuma saitin da kasuwar canjin kuɗi ta ɗauka yanzu, inda Naira ke ci gaba da samun tagomashi.

Cardoso ya ce wannan ci gaban ya taimaka wajen daidaita tsammanin kasuwa da kuma rage hauhawar farashi.

Tags: CBNOlayemiCardoso
Previous Post

Ba mu biya kuɗin fansa don a sako ɗaliban Neja ba – Gwamnatin Tarayya

Next Post

Zargin yi wa wayar Ribaɗu kutse: Kotu ta sanya ranar 23 ga Afrilu domin gurfanar da El-Rufai

Related Posts

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa

May 3, 2026
Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda

May 1, 2026
Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna

May 1, 2026
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Juyin Zamani: Yadda CBN ke ƙarfafa wa ɗalibai koyon ilmin sarrafa kuɗi, yayin da tattalin arziki ke sauyawa a zamanance 

April 30, 2026
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ke ta ƙoƙarin daƙile malejin hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100

April 29, 2026
Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna

April 27, 2026
Next Post
El-Rufai ya rubuta wa Ribaɗu takardar neman ƙarin haske kan zargin shigo da ‘guba mai haɗari’

Zargin yi wa wayar Ribaɗu kutse: Kotu ta sanya ranar 23 ga Afrilu domin gurfanar da El-Rufai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!