• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sabon Sufeto-Janar Olatunji Disu ya karɓi ragamar aiki: Shin wanene shi?

Tarihin sabon IGP

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
February 25, 2026
in Tsaro
A A
0
Sabon Sufeto-Janar Olatunji Disu ya karɓi ragamar aiki: Shin wanene shi?
Daga hagu: Muƙaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya karɓi ragamar aiki a matsayin Sufeto Janar na ’Yan Sanda ɗan ƙasa na 23.

Daga hagu: Muƙaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya karɓi ragamar aiki a matsayin Sufeto Janar na ’Yan Sanda ɗan ƙasa na 23.

Muƙaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya karɓi ragamar aiki a matsayin Sufeto Janar na ’Yan Sanda ɗan ƙasa na 23.

Ya karɓi muƙamin ne daga hannun Dakta Kayode Adeolu Egbetokun wanda ya yi aiki a matsayin Sufeto Janar na ’Yan Sanda na ƙasa na asali na 22 daga ranar 19 ga Yuni, 2023 zuwa ranar 24 ga Fabrairu, 2026.

Disu, wanda aka haifa a ranar 13 ga Afrilu, 1966, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Lagos Island ne a Jihar Legas.

Takardun karatun sa sun haɗa da:

  • Digiri na biyu (MSc) a fannin Kasuwanci (Entrepreneurship), jami’ar NOUN (2023);
  • Digiri na biyu (MSc) a fannin Ilimin Laifuka, Tsaro da Ilimin Halayyar Shari’a, LASU (2022);
  • Babbar Diploma a Binciken Laifuffuka da Hangen Nesa na Laifi (Forensic Investigation and Criminal Intelligence), UNILAG (2019);
  • Digiri na biyu (MSc) a fannin Gudanar da Harkokin Jama’a (Public Administration), Jami’ar Adekunle Ajasin (2010);
  • Difloma (PGD) a Harkokin Ƙasashen Waje da Nazarin Dabarun Tsaro, LASU (2000);
  • Digiri na farko (B.A.) Turanci (English), LASU (1990).

Ya shiga aikin ’yan sanda a matsayin Cadet Assistant Superintendent of Police a ranar 18 ga Mayu, 1992, kuma yana kawo gogewa mai yawa a fannonin aiki, bincike, tattara bayanan sirri da gudanarwa, wanda ya samo daga dogon lokaci na hidima mai daraja a muƙamai daban-daban na dabarun tsaro a faɗin ƙasar nan.

Kafin wannan sabon naɗi nasa, shi ne Mataimakin Sufeto-Janar (AIG), a hedikwatar si’aidi (FCID) Annex, da ke Alagbon, a Legas.

Muƙaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu (a hagu), jim kaɗan bayan ya karɓi ragamar shugabanci

Wasu daga cikin muƙaman da ya riƙe a baya sun haɗa da:

  • Assistant Inspector-General of Police (AIG), Special Protection Unit (SPU), Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda, Abuja
  • Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja
  • Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ribas
  • Kwamishinan ’Yan Sanda, mai kula da Gudanarwa da Bayanai, Force Intelligence Bureau (FIB)
  • Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, Shugaban Intelligence Response Team (IRT)
  • Kwamanda, Rapid Response Squad (RRS) Legas, 2015 – 2021
  • ACP, Sashen Binciken Laifuffuka, Jihar Ribas
  • Shugaban Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane, Jihar Ribas
  • Shugaban Sashen Yaƙi da Fashi da Makamin na Musamman (SARS) a Jihohin Ondo da Oyo, 2011 – 2014
  • DPO, Jihar Ondo, 2007 – 2013
  • Shugaban Horaswa, Sashen Ayyukan Zaman Lafiya na ’Yan Sandan Nijeriya
  • Malamin Horaswa, Kwalejin ’Yan Sandan Nijeriya, Kano
  • ADC ga tsohon Gwamnan Jihar Legas
  • Shugaban Sashen Yaƙi da Zamba, Sashen Binciken Laifuffuka na Jihar Katsina, 1993 – 1998.

Disu memba ne a ƙungiyoyi da hukumomi masu yawa da suka haɗa da: International Academy of Forensics; National Association of Investigative Specialists (NAIS), Amurka; Nigerian Institute of Public Relations (NIPR); Chartered Institute of Personnel Management (CIPM); da kuma International Association of Chiefs of Police.

Ya jagoranci rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta farko zuwa aikin African Union Mission in Sudan (AMIS) domin daƙile rikicin Darfur, Sudan, a shekarar 2005.

Ya taɓa zama Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Sanda Masu Wasan Judo ta Nijeriya (Nigeria Police Judo Association), kuma ya samu bel baƙi na uku a wasan Judo, tare da lashe lambobin yabo da dama, ciki har da lambar azurfa a gasar US Open Judo ta 2022.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Muƙaddashin ACP Benjamin Hundeyin, ya bayyana a cikin sanarwar manema labarai a yau Laraba cewa tarihin jagorancin sabon IGP ɗin da ƙwarewar sa da sadaukarwar sa ga aiki suna nuna cikakken shirin sa na jagorantar Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya a wannan muhimmin lokaci.

Ya ce: “Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya na mika godiya ta musamman ga tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, bisa gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa, zamani da ƙarfafa rundunar.

“Sabon Muƙaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya tabbatar wa jami’ai da ma’aikatan rundunar, masu ruwa da tsaki da al’umma baki ɗaya cewa zai ci gaba da ƙarfafa gyare-gyaren da aka fara, inganta tsaron cikin gida, ƙarfafa haɗin gwiwa da al’umma, tare da cika nauyin kare rayuka da dukiyoyi bisa ƙa’idojin duniya.

“Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya na roƙon ci gaba da goyon baya da haɗin kan jama’a yayin da sabon shugabanci ke aiki domin ƙara ƙwarewa, ladabi da ingantaccen hidima.”

Tags: 'yansandaKayodeAdeoluEgbetokunOlatunjiRilwanDisuragamashugabanci
Previous Post

Zargin yi wa wayar Ribaɗu kutse: Kotu ta sanya ranar 23 ga Afrilu domin gurfanar da El-Rufai

Next Post

Tawagar Google ta ziyarci Minista Idris a ofis

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Next Post
Tawagar Google ta ziyarci Minista Idris a ofis

Tawagar Google ta ziyarci Minista Idris a ofis

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!