• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Wani mutum ya yi wa ladani yankan rago cikin masallaci a Kano, shi kuma jama’a sun kashe shi

ALI KANO by ALI KANO
December 15, 2025
in Tsaro
A A
0
Wani mutum ya yi wa ladani yankan rago cikin masallaci a Kano, shi kuma jama’a sun kashe shi

 

Sallar asuba a wani masallaci a birnin Kano ta rikiɗe zuwa zubar da jini a safiyar yau Litinin, inda aka kashe wani dattijo ladani a cikin masallaci, lamarin da ya tayar da hankali da firgici.

An bayyana mamacin da suna Ladan Zubairu, wanda aka kashe a Masallacin Yusuf Garko da ke yankin unguwar Maraba a Kano, jim kaɗan bayan ya yi kiran sallar asuba na farko.

Wanda ake zargi, wanda ba a bayyana sunan sa ba nan take, ya shiga masallacin ɗauke da makami mai kaifi, ya kai wa limamin hari yayin da yake zaune a cikin masallacin.

A cewar shaidu, Zubairu ya kammala kiran sallah na farko, kuma kamar yadda ya saba, sai ya zauna na ɗan lokaci yana yin addu’o’i yana jiran kiran sallah na biyu, a nan ne maharin ya afka masa.

Da yake zantawa da ’yan jarida, ɗan mamacin, Isa Ƙasim, ya ba da labarin abin da ya faru mai tayar da hankali, ya ce: “Baban mu ya fita da sassafe domin kiran sallah. Bayan kiran farko, yakan zauna yana yin addu’a kafin na biyu. Yana zaune sai wani ya shiga masallacin, ya kama shi ya yanka shi. An farɗe yanke wuyan sa.”

Kisan gillar ya fusata mazauna yankin nan take. Rahotanni sun nuna cewa matasa sun tashi tsaye, suka bi wanda ake zargin ta kan titunan da ke kusa, daga bisani suka kama shi.

Ƙasim ya tabbatar da cewa jama’a cikin fushi sun kashe wanda ake zargin jim kaɗan bayan harin.

“Da yardar Allah, maharin bai tsira ba. Mutanen unguwa sun bi shi, suka kama shi suka kashe shi,” inji shi.

Abin da ya ƙara tayar da hankali shi ne yadda daga bisani mazauna yankin suka gano cewa ana zargin maharin yana ɗauke da sassan wuyan limamin da aka yanke, an naɗe su cikin leda a aljihun sa, lamarin da ya ƙara tsananta tashin hankali a unguwar.

Bayan haka, rahotanni sun ce matasa cikin fushi sun banka wa gidan wanda ake zargin wuta, abin da ya jawo firgici sosai tare da tilasta wa jama’a tserewa daga gidajen su kafin jami’an tsaro su isa domin dawo da doka da oda.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta tura jami’ai yankin domin hana ƙarin taɓarɓarewar tsaro.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Litinin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce jami’an tsaro sun yi gaggawar shiga tsakani domin kwantar da hankula.

“Jami’an mu sun shiga tsakani da sauri domin dawo da zaman lafiya tare da hana ƙarin rikici. Yanzu al’amura sun dawo daidai a unguwar Maraba,” inji shi.

Kiyawa ya bayyana cewa an kwashe gawar limamin da aka kashe da kuma ta wanda ake zargi aka kai su Asibitin Koyarwa na Mohammed Abdullahi Wase domin yin binciken gawarwaki.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya jawo kisan da kuma kisan da jama’a suka yi daga baya.

“Muna da niyyar tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin doka,” inji kakakin ’yan sanda.

Hukumomi sun yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalin su tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen binciken da ake yi.

Lamarin ya sake tayar da damuwa kan ƙaruwar tashin hankali, hukuncin jama’a da kuma tsaro a wuraren ibada a wasu sassan ƙasar nan.

Tags: 'yan sandaKanokisaLadanmasallaci
Previous Post

CBN ya umurci masu PoS su bi hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe nan da kwana 30

Next Post

Turnuƙu kan fetur: Ɗangote ya fallasa cikakkun bayanai kan makarantun da ’ya’yan shugaban NMDPRA suka halarta a Switzerland

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa
Tsaro

’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa

May 8, 2026
Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
Next Post
Turnuƙu kan fetur: Ɗangote ya fallasa cikakkun bayanai kan makarantun da ’ya’yan shugaban NMDPRA suka halarta a Switzerland

Turnuƙu kan fetur: Ɗangote ya fallasa cikakkun bayanai kan makarantun da ’ya’yan shugaban NMDPRA suka halarta a Switzerland

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!