• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci masu PoS su bi hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe nan da kwana 30

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
December 14, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya umurci masu PoS su bi hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe nan da kwana 30
Hadahadar kuɗi ta hanyar POS

Hadahadar kuɗi ta hanyar POS

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umurci dukkan masu hadahadar mu’amalar kuɗaɗe da Point of Sale (PoS) da kuma masu ba da sabis na biyan kuɗi da su tabbatar da haɗa na’urar PoS da lambar sirrin shaidar aikawa da kuɗi daga wani banki zuwa wani, wato Nigeria Inter-Bank Settlement System (NIBSS) da kuma lambar bai-ɗaya mai tabbatar da shigar kuɗi asusun da aka tura shi cikin gaggawa, wato Unified Payment Services Limited (UPSL) nan da kwanaki 30.

CBN ya ce an fito da wannan sabon umarni na baya-bayan nan ne domin magance yawaitar samun matsalolin tangarɗar kasawa ko ƙin shigar kuɗaɗe cikin asusun da aka tura su nan take, da ma sauran cikas ɗin da ake fuskanta yayin mu’amaloli a tsarin biyan kuɗi a ƙasar nan.

Wannan umurni yana cikin wata sanarwa mai taken PSS/DIR/PUB/CIR/001/002, wadda Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi, Rakiya Yusuf, ta sanya wa hannu.

Umarnin ya shafi dukkan masu karɓar biyan kuɗi masu sarrafa hadahadar kuɗi, masu tara sabis na na’urorin biyan kuɗi, da sauran masu ba da sabis da ke aiki a Nijeriya.

A cewar babban bankin, wannan tsari ya ginu ne bisa shawarar da CBN ya yanke a watan Satumba, 2024 na dakatar da dogaro da hanyar dogaro da tsarin mu’amala guda ɗaya, wanda bankin ya ce yana da babban tasiri wajen haddasa yawan katsewar sabis a tsarin biyan kuɗi na zamani a Nijeriya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a ƙarƙashin sabon tsari, dukkan masu PoS dole ne su riƙa haɗin kai da duka kamfanonin da aka ba lasisin tara sabis na na’urorin biyan kuɗi, wato NIBSS da UPSL, tare da daidaita tsarin su yadda zai iya sauya hanyar kasa wucewar kuɗin da aka tura kai-tsaye, wato ‘automatic failover’, idan wata hanya ta samu matsala. Wannan zai tabbatar da cewa ana ci gaba da mu’amala ba tare da tsaiko ba idan ɗaya daga cikin hanyoyin ta fadi.

CBN ya bayyana cewa wannan mataki na da nufin rage yawan gazawar turawa da shigar kuɗaɗe daga wannan banki zuwa wani banki ta hanyar amfani da PoS da ke cutar da ‘yan kasuwa, masu saye da sayarwa, har ma da kamfanoni, musamman a sashen kasuwanci na dillalai da na kasuwar gargajiya, inda na’urorin PoS suke zama babbar hanyar biyan kuɗi.

Domin ƙarfafa juriyar tsarin da kuma tabbatar da bin doka, an umurci NIBSS da UPSL da su riƙa gudanar da gwaje-gwajen tsarin akai-akai tare da cibiyoyin kuɗi, sannan su miƙa rahoton sakamakon gwaje-gwajen ga CBN.

Haka kuma, kamfanonin mu’amalar kuɗi biyu guda biyu dole ne su riƙa ba bankuna sanarwa kai-tsaye idan tsarin ya samu tangarda, tare da gabatar da cikakken rahoton abin da ya faru ga Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi cikin sa’o’i 24, ciki har da musabbabin matsalar da matakan gyara da aka ɗauka.

Wa’adin bin wannan umarni na kwanaki 30, wanda zai ƙare a tsakiyar watan Janairun 2026, ya sanya babban nauyi a kan masana’antar da ke sarrafa miliyoyin hadahadar kuɗaɗe a kowace rana, yayin da Nijeriya ke hanzarta sauyawa zuwa tsarin hadahadar kuɗi ta zamani, wato dijital.

Gazawar mu’amalolin PoS ta ci gaba da zama babbar matsala duk da matakan da CBN ta taɓa ɗauka a baya, ciki har da ƙaddamar da buƙatar geo-tagging a watan Agusta.

Duk da cewa yawancin masu ruwa da tsaki a masana’antar sun yaba da umarnin haɗin kai a matsayin muhimmin mataki na daidaita ginshiƙin tsarin biyan kuɗi.

Tags: CBNPOS
Previous Post

Tinubu ya naɗa Yakubu da ministoci shida a kwamitin warware bashin naira tiriliyan 1.5 da ‘yan kwangila ke bin gwamnati

Next Post

Wani mutum ya yi wa ladani yankan rago cikin masallaci a Kano, shi kuma jama’a sun kashe shi

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Wani mutum ya yi wa ladani yankan rago cikin masallaci a Kano, shi kuma jama’a sun kashe shi

Wani mutum ya yi wa ladani yankan rago cikin masallaci a Kano, shi kuma jama’a sun kashe shi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!