Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afrika kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya sake fitar da wasu bayanai domin ƙarfafa zargin da yake yi wa Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Cikin Teku ta Nijeriya (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed, cewa ya kashe miliyoyin daloli wajen ilimintar da ’ya’yan sa a ƙasashen waje.
A cikin wata talla da ya wallafa a wasu manyan jaridun ƙasar nan, Ɗangote ya yi iƙirarin cewa Ahmed ya kashe zunzurutun kuɗi kimanin dala miliyan 5 wajen karatun sakandare na ’ya’yan sa huɗu a ƙasar Switzerland tsawon shekaru shida.
Tun da farko, attajirin ya zargi shugaban NMDPRA ɗin da biyan kusan dala miliyan 5 ga wata makarantar sakandare a Switzerland domin karatun ’ya’yan nasa, yana kiran wannan kashe-kashen a matsayin “ta’asar tattalin arziƙi da cin hanci,” zargin da ya jawo muhawara da tsakanin jama’a.
A sabuwar tallar da ya buga, Ɗangote ya gabatar da jadawalin kuɗaɗen da ake zargin an kashe, tare da ambato sunayen ’ya’yan da abin ya shafa, wato Faisal Farouk, Farouk Juniyo, Ashraf Farouk da Farhana Farouk.
A cewar tallar, ’ya’yan sun halarci wasu daga cikin manyan makarantu mafi tsada kuma na masu kuɗi a Switzerland, ciki har da Montreux School, Aiglon College, Institut Le Rosey da La Garenne International School, a tsawon shekaru shida.
Ɗangote ya lissafta abin da ya kira ƙiyasin kuɗaɗen makaranta, wurin kwana, kulawa, da tafiye-tafiye na ƙasa da ƙasa.
Ya ce kuɗin makaranta, jirgi da kulawa a kowace shekara ga kowane yaro ya kai kusan dala 200,000, wanda ke nufin jimillar kusan dala 800,000 a shekara ga ’ya’yan huɗu.
Ya ƙara da cewa a cikin shekaru shida, jimillar kuɗin more rayuwa da tafiye-tafiye ta jirgi ta kai dala miliyan 1.2 ga kowane yaro, wanda ya zama dala miliyan 4.8 ga ’ya’yan huɗu baki ɗaya.
Bisa wannan ƙididdiga, Ɗangote ya kammala da cewa jimillar kuɗin karatun sakandare da abubuwan da suka shafi kulawa ga ’ya’yan ta kai kusan dala miliyan 5.
Baya ga karatun sakandare, ɗan kasuwar ya kuma jero abin da ya kira kuɗaɗen karatun jami’a da Ahmed ya kashe wa ’ya’yan sa.
A cewar Ɗangote, matsakaicin kuɗin makaranta, more rayuwa, kuɗin jirgi da sauran ƙananan kuɗaɗe a matakin jami’a ga kowane yaro ya kai kusan dala 125,000 a shekara tsawon shekaru huɗu. Wannan, inji shi, ya kai dala 500,000 ga kowane yaro, ko kuma jimillar dala miliyan 2 ga ’ya’yan huɗu baki ɗaya.
Ya kuma ware ɗaya daga cikin ’ya’yan, Faisal Farouk, yana cewa kwanan nan ya kammala karatun digirin MBA (Master of Business Administration) a Jami’ar Harvard a shekarar 2025.
“Faisal ya kammala MBA na Harvard na shekarar 2025 da dala 150,000, tare da ƙarin dala 60,000 don kulawa, tikitin jirgi da sauran ƙananan kuɗaɗe, wanda ya sa jimillar abin da aka kashe a shekarar 2025 kaɗai ya kai dala 210,000,” inji Ɗangote.
Attajirin ya yi nuni da cewa ’yan Nijeriya suna da haƙƙin yin tambaya kan asalin kuɗin da aka yi irin wannan watandar da su, musamman ganin matsayin Ahmed na jami’in gwamnati.
Ya kwatanta wannan zargin kashe-kashen kuɗin da halin tattalin arziƙin da ’yan Nijeriya da dama suke ciki, musamman a Jihar Sokoto inda Ahmed ya fito, inda, a cewar sa, iyaye da yawa suke fama da wahalar biyan kuɗin makaranta da bai wuce ₦10,000 ba ga ’ya’yan su.
Ya jaddada cewa gaskiya da riƙon amana suna buƙatar a ba da bayani a fili idan manyan jami’an gwamnati suna da salon rayuwa da kashe kuɗin da ba su dace da abin da aka sani na albashin su ba.
A lokacin haɗa wannan rahoto dai Farouk Ahmed da hukumar NMDPRA ba su ce uffan ba dangane da cikakkun zarge-zargen da aka wallafa a tallar ta Ɗangote.






