Nijeriya tare da ƙasashe 144 sun kaɗa ƙuri’a a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya domin bai wa Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, damar yin jawabi ta hanyar bidiyo a babban taron majalisar (UNGA) bayan Amurka ta ƙi bada biza ga tawagar sa.
An kaɗa ƙuri’ar ne a birnin New York, inda aka samu ƙuri’u 145 na amincewa, ƙasashe biyar suka ƙi (ciki har da Amurka da Isra’ila), yayin da ƙasashe shida suka ƙaurace.

Wannan matakin zai bai wa Abbas damar aiko da jawabin sa da aka riga aka ɗauka ta bidiyo, wanda wani wakilin Falasɗinu a New York zai gabatar a ɗakin taron.
Haka kuma an amince a yi amfani da wannan tsari na jawabin bidiyo ko ta haɗin kai-tsaye (live) a wasu muhimman taruka na majalisar, amma a abin da ya shafi zaman majalisar karo na 80 kawai.







