Rundunar sojin Isra’ila ta ba da tabbaci a yau Litinin cewa hoton nan da ke yawo a soshiyal midiya ke nuna wani daga sojan ta a kudancin Lebanon yana bugun gunkin Yesu Almasihu da ƙatuwar guduma gaskiya ne.
Hoton ya nuna wani sojan Isra’ila yana amfani da ƙatuwar guduma wajen bugun kan wani gunki na Yesu da aka gicciye wanda ya faɗo daga kan gicciye.
Gunkin yana cikin ƙauyen Kiristoci na Debl da ke kudancin Lebanon, kusa da kan iyakar Isra’ila, kamar yadda ƙaramar hukumar yankin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, amma jami’ai ba su tabbatar ko an lalata shi ba.
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafin ta na X a yau Litinin cewa tana kallon lamarin da “matuƙar damuwa”, ta ƙara da cewa “abin da sojan ya aikata ya saɓa wa ɗabi’u da ƙa’idojin da ake buƙata daga sojojin ta”.
Rundunar ta ce: “Bayan kammala binciken farko dangane da hoton da aka wallafa a yau wanda ke nuna wani soja na IDF yana lalata wata alamar addinin Kirista, an tabbatar da cewa hoton ya nuna wani soja na IDF da ke aiki a kudancin Lebanon.”
Ta ƙara da cewa rundunar yankin Arewa ce ke binciken lamarin, kuma a halin yanzu ana magance shi ta hanyar tsarin jagoranci.
Rundunar ta ce za a ɗauki “matakan da suka dace” kan waɗanda abin ya shafa, amma ba ta yi ƙarin bayani ba.
Ta kuma ce tana aiki tare da al’ummar yankin domin “mayar da gunkin zuwa wurin sa”.
Ministan harkokin wajen Isra’ila, Gideon Saar, ya yi tir da abin da ya kira “abin kunya da wulaƙanci”.
“Ina da yaƙinin cewa za a ɗauki matakan ladabtarwa masu tsauri kan duk wanda ya aikata wannan mummunan aiki,” inji shi a shafin sa na X.
“Muna neman afuwa kan wannan lamari da kuma ga duk wani Kirista da wannan abu ya ɓata masa rai.”






