Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana a yau Juma’a cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce, yayin da ya fitar da sakamakon duba lafiyar sa na shekara-shekara.
Netanyahu mai shekaru 76 ya ce ya jinkirta fitar da rahoton lafiyar sa na shekara-shekara—wanda ya nuna an gano yana ɗauke da cutar sankara a karon farko—na tsawon watanni biyu domin kada Iran ta yi amfani da shi a matsayin farfaganda.
Jagoran da ya fi kowa daɗewa kan mulki a tarihin Isra’ila ya yi tiyatar kumburin ‘ya’yan maraina a watan Disamban 2024, aikin da Ofishin Firayim Minista ya bayyana shi a bainar jama’a a lokacin. A sabon binciken da aka yi bayan tiyatar, Netanyahu ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a kafafen sada zumunta cewa likitoci sun gano wani mugun ƙari (tumor) mai cutar sankara a cikin ‘ya’yan marainan sa, wanda girman sa bai kai santimita guda ba.
Ofishin Firayim Ministan ya kuma fitar da wasiƙu biyu daga likitocin sa domin bayyana wannan bayani a kafafen sada zumunta. “An gano wannan tun da wuri, kuma ƙari ne ƙanƙani sosai, ba tare da yaɗuwa zuwa wasu sassan jiki ba, kamar yadda sauran gwaje-gwaje suka tabbatar ba tare da wata shakka ba,” inji ɗaya daga cikin wasiƙun.
Bai bayyana lokacin da aka yi binciken na ƙarshe ba, amma wata majiya daga Isra’ila da ta san batun ta shaida wa CNN cewa an gano cutar watanni da dama da suka gabata. A cewar majiyar, Netanyahu ya fara shan maganin radiation kusan watanni biyu da rabi da suka wuce, kuma kwanan nan ya kammala jinyar.
Netanyahu ya ce ya yanke shawarar yin maganin radiation na musamman, kuma “gurbin cutar ya ɓace gaba ɗaya.”
“Alhamdu lillah, ina cikin ƙoshin lafiya,” Netanyahu ya wallafa a kafafen sada zumunta. “Na samu wata ƙaramar matsalar lafiya da ta shafi ‘ya’yan maraina na, kuma an yi maganin ta gaba ɗaya.”






