A yau Lahadi Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja domin wakiltar Nijeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 80 da za a gudanar a birnin New York da ke Amurka, daga gobe Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28 ga watan.
Wannan na zuwa ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya bayyana a wata sanarwa a Abuja.
A cewar sanarwar, Shettima zai halarci taron murnar cika shekara 80 da kafa Majalisar Ɗinkin Duniya a gobe, sannan daga ranar Talata 23 zuwa Lahadi 28 zai shiga tattaunawar manyan shugabanni a zauren babban taron.
Haka kuma a ranar Laraba, 24 ga Satumba ne zai gabatar da jawabin ƙasa na Nijeriya tsakanin ƙarfe 3 zuwa 9 na dare agogon New York.

Bugu da ƙari, Shettima zai shiga taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya zai jagoranta a ranar 24 ga Satumba, inda Nijeriya za ta sanar da sababbin manufofin ta bisa Yarjejeniyar Paris.
Haka kuma zai halarci taron manyan shugabanni kan samar da gidaje masu araha da shugaban Kenya zai shirya.
Bayan kammala taron majalisar, Shettima zai zarce Frankfurt a ƙasar Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutche kafin ya dawo gida Nijeriya.







