Wani mutum ya harbe yara takwas har lahira, bakwai daga cikin su ‘ya’yan sa ne, a gidaje uku da ke garin Shreveport na ƙasar Amurka da safiyar jiya Lahadi, inji ‘yan sanda. Wannan ya zama harin bindiga mafi muni a ƙasar tun watan Janairu na 2024.
Yaran da aka kashe sun haɗa da maza uku da mata biyar, masu shekaru tsakanin 3 zuwa 11, inji ofishin mai binciken gawa na Caddo Parish ga CNN. Sun haɗa da ‘yan’uwa guda bakwai da kuma ɗan’uwan su ɗaya, inji ofishin. Tun da farko ‘yan sanda sun ce shekarun su sun kai daga 1 zuwa 14.
Ofishin mai binciken gawa ya bayyana sunayen waɗanda suka mutu kamar haka: Jayla Elkins (3), Shayla Elkins (5), Kayla Pugh (6), Layla Pugh (7), Markaydon Pugh (10), Sariahh Snow (11), Khedarrion Snow (6), da Braylon Snow (5).
Jami’in ‘yan sandan Shreveport, Cpl. Chris Bordelon, ya bayyana sunan wanda ya kai harin a matsayin Shamar Elkins, kuma ya shaida wa tashar KSLA cewa harin “na cikin gida ne” (domestic). A cewar rahotannin baya, Elkins yana da shekaru 31.
Wani yaro mai shekaru 13 ya ji rauni bayan ya tsere daga gida ya yi tsalle daga kan rufi, inji Bordelon. Ya samu karayar ƙashi kaɗan amma ana sa ran zai warke, inji shi.
Wasu daga cikin yaran sun yi ƙoƙarin tserewa ta ƙofar baya yayin harin, inji ‘yar majalisar jihar, Tammy Phelps, a wani taron manema labarai.
Har ila yau, mata biyu manya sun samu harbi a harin, inji Bordelon. Matar Elkins, wadda ita ce uwar ‘ya’yan sa, ita ce aka fara harbi kuma ta samu munanan raunuka.
Daga nan Elkins ya tafi wani gida daban inda ya harbe yara takwas da wata mace. Wannan matar, wadda ita ce uwar yaro na takwas da aka kashe, tana cikin mawuyacin hali mai barazana ga rayuwa, inji shi.
An taɓa kama Elkins a 2019 kan wani laifin samun sa da bindiga, inji rahoton ‘yan sanda. Bayan wani mutum ya nuna masa bindiga daga cikin mota, Elkins ya mayar da martani ta hanyar harba harsasai biyar a kusa da makaranta.
Haka kuma ya taɓa yin aikin soja a rundunar Louisiana Army National Guard na tsawon shekaru bakwai har zuwa Agusta 2020, inji rundunar sojin Amurka. Ba a tura shi zuwa yaƙi wata ƙasa ba.
‘Yan sanda dai sun harbe shi har lahira a jiya bayan ya ƙwace mota ya kuma ja su cikin wani tseren mota zuwa wani yanki na kusa, inji Bordelon. Rundunar ‘yan sandan Jihar Louisiana na binciken lamarin.
“Wannan lamari ya girgiza dukkanin birnin,” inji magajin garin Shreveport, Tom Arceneaux. “Ya shafi kowa.”
A bana kaɗai, an samu aƙalla hare-haren bindiga 114 a Amurka, inji hukumar Gun Violence Archive, wadda ta ɗauki harin bindiga a matsayin inda aka harbi mutane huɗu ko fiye, ba tare da lissafa mai harin ba.
Birnin Shreveport, wanda ke kusan mil 250 arewa maso yammacin Baton Rouge, yana da kusan mazauna 180,000. Fiye da kashi 30% na kisan kai a birnin yana da nasaba da rikicin cikin gida, inji ɗan majalisar birni Grayson Boucher.

‘Wuri mai firgitarwa’
‘Yan sanda sun amsa kiran harbe-harbe a yankin Cedar Grove da ke Shreveport da misalin ƙarfe 6 na safe, inda suka tarar da gawarwaki a gidaje biyu a kan titin West 79th Street da kuma gida na uku a Harrison Street, inji Bordelon.
“Wannan babban wuri ne mai ɗauke da gawar yara da dama,” inji shi.
Magajin gari Arceneaux ya bayyana wurin a matsayin “mai matuƙar firgitarwa.”
Waɗannan hare-haren sun kai jimillar kisan kai na 8 zuwa 15 a Shreveport da Caddo Parish a bana, inji ofishin mai binciken gawa.
Kyamarar tsaro ta wani maƙwabci ta ɗauki bidiyo inda ake ganin wanda ya kai harin yana gudu zuwa wani shagon gyaran tayoyi, inji Associated Press. Wata maƙwabciya, Liza Demming, ta ce ta gan shi yana gudu daga gidan.
Ta kuma ce daga baya ta fita waje ta ga gawar wani yaro da aka rufe a saman rufin gidan.
Bala’i da ya wuce wurin da ya faru
‘Yar majalisar birni Tabatha H. Taylor ta fashe da kuka yayin da take magana kan lamarin, tana faɗin, “Ina roƙon al’umma tare da addu’a, da dukkan masu ba da shawara kan lafiyar ƙwaƙwalwa da masu taimako: wannan iyali da wannan al’umma na buƙatar ku. Ni ma ina buƙatar ku. Ta yaya za mu iya jure wannan?”
Arceneaux ya kira lamarin “abin takaici mai tsanani,” yana mai cewa wataƙila shi ne mafi muni a tarihin birnin.
“Zuciya ta ta cika da alhini. Ba zan iya fahimtar yadda irin wannan zai faru ba,” inji shugaban ‘yan sandan Shreveport, Wayne Smith.
Shugaban Majalisar Wakilan Amurka, Mike Johnson, wanda ke wakiltar yankin Shreveport, ya bayyana kisan a matsayin “abin tausayi sosai.”
“Muna jajanta wa waɗanda suka rasa rayukan su, iyalan su da al’ummar mu ta Shreveport a cikin addu’o’i a wannan lokaci mai wahala,” inji shi.
Shugaban makarantu na Caddo Parish, Keith Burton, ya ce dole ne al’umma ta “kula da yaran mu, ta tallafa wa iyalai, kuma ta tsaya tare da malamai da jami’an agaji da ke ɗaukar nauyin wannan lokaci mai wuya.”
Arceneaux ya ce wannan bala’i ya wuce wurin da ya faru kawai.
“Irin waɗannan lokuta suna barin tabo mai ɗorewa — a zukatan mu, a tunanin mu, da kuma a yadda muke jin tsaron mu,” inji magajin garin.
Rahoto daga: CNN






