• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun kama wanda ake zargin ɗan ƙunar baƙin wake ne, sun tare kayayyakin haɗa bam a Borno

ALI KANO by ALI KANO
December 30, 2025
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun kama wanda ake zargin ɗan ƙunar baƙin wake ne, sun tare kayayyakin haɗa bam a Borno
Sojoji suna zargin Abubakar Mustapha ɗan ƙunar baƙin wake ne

Sojoji suna zargin Abubakar Mustapha ɗan ƙunar baƙin wake ne

Rundunar Sojin Nijeriya ta Joint Task Force North East, Operation Haɗin Kai, ta bayyana cewa ta kama wani da ake zargin ɗan kunar baƙin wake ne tare da kame wasu kayayyaki da ake shirin amfani da su wajen ƙera na’urorin fashewa na hannu (IEDs) a Jihar Borno.

Jami’in yaɗa labarai na Hedikwatar Joint Task Force (Arewa Maso Gabas) Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce kamen ya biyo bayan ci gaba da gudanar da haɗin gwiwar ayyukan tsaro da kuma tattara sahihin bayanan sirri domin tabbatar da tsaron garin Banki a Karamar Hukumar Bama.

Ayyukan sun gudana ne ƙarƙashin jagorancin dakarun Bataliya ta 152 Task Force, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Ya ce: “Da misalin ƙarfe 1740 na ranar Litinin, 29 ga Disamba, 2025, jami’an da aka tura wajen Babban Masallacin Banki sun kama wani da ake zargin ɗan ƙunar baƙin wake ne mai suna Abubakar Mustapha.

“An same shi ɗauke da sassan IEDs da aka riga aka shirya, abin da ke nuna cewa yana da niyyar kai hari nan take.”

A cewar sa, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bama ne, kuma an gano yana ɗauke da wasu ƙarin kayayyakin da ke da alaƙa da ayyukan ta’addanci.

“Yanzu haka ana yi masa cikakken bincike domin gano masu ɗaukar nauyin sa, abokan hulɗar sa, da kuma yiwuwar alaƙar sa da ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ke aiki a yankin,” inji Uba.

Kayayyakin da ake shirin amfani da su wajen ƙera na’urorin fashewa (IEDs) da aka ƙwato daga wani da ake zargi a garin Banki, Ƙaramar Hukumar Bama, Jihar Borno
Wasu daga cikin ƙarin kayayyakin da sojoji suka ƙwato

A wani lamari irin wannan, dakarun da aka jibge a ƙofar iyakar Kamaru da Nijeriya sun tare wata mota ƙirar Fijo da ke ɗauke da buhuna shida na takin uriya, wanda wani muhimmin sinadari ne da ake yawan amfani da shi wajen ƙera makaman IED.

Uba ya ce nan take aka ƙwace motar da takin uriya ɗin tare da kai su hannun sojoji.

Ya ƙara da cewa, ci gaba da amfani da bayanan sirri da aka samu daga wannan tarewa ya kai ga kama dillalin takin, tare da ƙwato ƙarin buhuna shida na uriya, wanda ya kai adadin abin da aka ƙwato gaba ɗaya zuwa buhuna goma sha biyu.

Dukkan waɗanda ake zargi da kuma kayayyakin da aka ƙwato suna hannun hukumomi domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan doka da suka dace, inji shi.

Buhuna shida na takin uriya da sojoji suka ƙwato daga wani da ake zargi

Kakakin rundunar ya ce: “Dakarun JTF NE OPHK na ci gaba da mamaye yankunan da ke ƙarƙashin kulawar su ta hanyar tsattsauran sintiri, ayyukan tsaro bisa bayanan sirri, da kuma kasancewa a yankuna ba tare da yankewa ba, domin hana ’yan ta’addan JAS/ISWAP saƙat da kuma daƙile hare-hare kan fararen hula da muhimman gine-gine.

“Ƙwarin gwiwa da ingancin faɗa na dakarun mu na nan daram kuma abin gamsarwa, yayin da ake ci gaba da aiwatar da ayyuka bisa ga umarnin dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a faɗin Arewa-maso-gabas.

“Sojoji suna sake tabbatar wa da al’umma aniyar su ta kare rayuka da dukiyoyi ba tare da sassauci ba, tare da roƙon jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci ga hukumomin tsaro domin tallafa wa ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake gudanarwa.”

Tags: BamabankiBornoLaftanar Kanal Sani Ubarashin tsarosojojita'addanci
Previous Post

Kotu ta tsare Malami, matar sa da ɗan sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

Next Post

2027: Peter Obi ya canza sheƙa daga LP zuwa ADC

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa
Tsaro

’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa

May 8, 2026
Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
Next Post
2027: Peter Obi ya canza sheƙa daga LP zuwa ADC

2027: Peter Obi ya canza sheƙa daga LP zuwa ADC

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!