Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana jajanta wa Sarkin Kaiama, Alhaji Mu’azu Shehu Omar (Kiyaru IV), a lokacin ziyarar
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci wata tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara domin jajanta wa al’ummar yankin da Gwamnan Jihar, Malam AbdulRahman AbdulRazaq, bisa mummunan harin ta’addanci da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar damuwa a ƙauyukan Nuku da Woro, inda harin ya jefa al’umma cikin alhini da firgici.
A jawabin sa ga jama’a da shugabannin yankin, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajirce wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.


Shettima ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa ya bayar da umurnin tura bataliyar Sojojin Nijeriya zuwa Kaiama domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ƙara da cewa dukkanin hukumomin tsaro suna aiki tare, kuma an ɗauki matakai na musamman domin kawar da barazanar rashin tsaro ba kawai a Kaiama ba, har da faɗin Jihar Kwara baki ɗaya.
Ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai, tare da yin addu’a domin zaman lafiyar yankin.

Gwamnan Jihar Kwara, Malam AbdulRahman AbdulRazaq, ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa gaggawar ɗaukar mataki, yana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen dawo da ƙwarin gwiwa da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.








