• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Za a buɗe kan iyakar Nijeriya da Nijar ta Tsamiya da ke Kebbi don cinikayya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
February 7, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Za a buɗe kan iyakar Nijeriya da Nijar ta Tsamiya da ke Kebbi don cinikayya
Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya (CG), Bashir Adewale Adeniyi

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya (CG), Bashir Adewale Adeniyi

Gwamnatin Tarayya ta amince da sake buɗe kan iyakar ƙasa ta Tsamiya da ke Jihar Kebbi domin ci gaba da gudanar da cinikayya, tare da tsauraran matakan tsaro da bin doka.

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya (CG), Bashir Adewale Adeniyi, shi ne ya bayyana hakan a yau Asabar yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a Birnin Kebbi, ciki har da ’yan kasuwa, masu safarar kaya da ’yan kasuwar albasa.

Adeniyi ya ce gwamnati ba ta yi kunnen uwar shegu da halin ƙuncin da aka shiga sakamakon rufe iyakokin ba, inda ya jaddada cewa an shafe lokaci ana tattaunawa a matakin diflomasiyya, tsaro da kwastam da maƙwaftan ƙasashen.

Ya bayyana cewa an karɓi wata tawaga ta gaggawa daga Hukumar Kwastam da Ƙungiyar Kasuwanci ta Jamhuriyar Nijar a Abuja, domin gaggauta warware cikas ɗin cinikayya.

“Ina farin cikin sanar da amincewar Shugaban Ƙasa cewa za a sake buɗe iyakar Tsamiya don ayyukan kasuwanci,” inji shi.

Shugaban Kwastam ɗin ya yi gargaɗin cewa buɗewar za ta gudana ne ƙarƙashin tsauraran ƙa’idojin tsaro, domin hana miyagu cin gajiyar hanyoyin kasuwanci.

Ya ce za a yi amfani da fasahar ICT wajen haɗa bayanan kwastam da na Nijar da Benin, tare da sa ido kan zirga-zirgar kaya. Ya kuma gargaɗi masu safara da kada su karkatar da kaya daga hanyar da aka amince da ita, yana mai cewa duk motar da aka kama za a ƙwace ta, tare da ɗaukar matakin shari’a.

Adeniyi ya ƙara da cewa bunƙasa al’ummomin da ke rayuwa a kan iyaka yana da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da haɗin kai.

Tags: BashirAdewaleAdeniyiiyakaKebbiKwastanNCSTsamiya
Previous Post

Gaba dai, gaba dai CBN: Ma’aunin yawan hadahadar masana’antu, kamfanoni da kasuwanci ya kai maki 55.7 a Janairu

Next Post

Shettima ya jajanta wa al’ummar Kaiama, ya jaddada ƙudirin Tinubu na dawo da zaman lafiya a faɗin Nijeriya

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Shettima ya jajanta wa al’ummar Kaiama, ya jaddada ƙudirin Tinubu na dawo da zaman lafiya a faɗin Nijeriya

Shettima ya jajanta wa al’ummar Kaiama, ya jaddada ƙudirin Tinubu na dawo da zaman lafiya a faɗin Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!