• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Bayan shekaru 37, Tinubu zai kai ziyarar musamman zuwa Birtaniya

ALI KANO by ALI KANO
February 8, 2026
in Labarai
A A
0
Bayan shekaru 37, Tinubu zai kai ziyarar musamman zuwa Birtaniya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da Sarki Charles na Uku

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da Sarki Charles na Uku

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana shirin kai wata muhimmiyar ziyara ta kwanaki biyu zuwa Birtaniya daga ranar 18 ga Maris, kamar yadda Fadar Buckingham ta Ingila ta tabbatar.

Hakan zai zama irin wannan ziyara ta farko da wani shugaban Nijeriya zai kai Ingila cikin shekaru 37.

Ziyarar, wadda ta zo ne bisa gayyatar Sarki Charles na Uku, ana kallon ta a matsayin wani babban mataki na diflomasiyya a dangantakar Nijeriya da Birtaniya, tare da nuna ƙarfi a fannin hulɗar ƙasashe ta hanyar “soft power”.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Asabar, Fadar Ingila ta bayyana cewa Tinubu zai tafi tare da maiɗakin sa, wato Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu.

Fadar ta ce za a ba da sanarwar cikakkun bayanai game da jadawalin ziyarar da sauran tarurrukan hukuma nan gaba kaɗan.

Wannan tafiya ita ce ziyara ta farko da wani shugaban Nijeriya zai kai Birtaniya tun shekarar 1989, lokacin da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya kai ziyara ta kwana huɗu bisa gayyatar marigayiya Sarauniya Elizabeth ta Biyu.

Kafin ziyarar Babangida, wasu shugabannin Nijeriya da suka kai irin wannan ziyarar sun haɗa da Janar Yakubu Gowon a cikin 1973 da Shugaba Shehu Shagari a 1981.

A cewar BBC, irin waɗannan ziyarce-ziyarce na musamman wata muhimmiyar hanya ce ta diflomasiyya, inda ake amfani da al’adun sarauta da martabar ta wajen ƙarfafa dangantaka da ƙasashen da ake da muhimmiyar hulɗa da su.

Ko da yake wannan ce ziyara ta farko da Tinubu zai kai Birtaniya a matsayin sa na shugaban ƙasa, ba shi ne karo na farko da ya gana da Sarki Charles ba.

Dukkanin shugabannin biyu sun hau mulki ne a watan Mayu 2023, kuma tun daga lokacin sun haɗu sau da dama.

A watan Nuwamba 2023, Tinubu ya gana da Sarkin na Birtaniya a gefen taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 28 (COP28) a birnin Dubai na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Daga baya Tinubu ya bayyana ganawar a matsayin wata muhimmiyar hanya ta ƙarfafa dangantakar Nijeriya da Birtaniya.

Haka kuma, a cikin Satumba 2024, Sarki Charles ya karɓi Shugaba Tinubu a Fadar Buckingham domin wata ganawa ta sirri.

A cewar mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga, tattaunawar ta mayar da hankali kan batutuwan duniya da na yankuna da ke da muhimmanci ga ɓangarorin biyu, musamman ƙalubalen sauyin yanayi da ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ko da yake har yanzu ba a bayyana cikakkiyar ajandar ziyarar ta Maris ba, masu bibiyar harkokin diflomasiyya na sa ran za a tattauna batutuwan kasuwanci, haɗin gwiwar tsaro, matakan yaƙi da sauyin yanayi, hijira, ilimi da bunƙasa matasa.

Sarki Charles dai ya daɗe yana da kusanci da Nijeriya, ta fuskar hulɗa ta ƙashin kai da ta hukumance.

Kafin hawan sa karagar mulki, ya kawo ziyara Nijeriya sau huɗu a matsayin sa na Yariman Wales a shekarun 1990, 1999, 2006 da 2018. Matar sa, Sarauniya Camilla, wadda a wancan lokaci ake kira Duchess ta Cornwall, ta rako shi a ziyarar shekarar 2018.

Sarkin ya kuma nuna ƙauna ga al’adun Nijeriya, musamman harshen Pidgin da kuma kiɗan Afrobeats.

A shekarar 2023, gidauniyar King’s Trust International, wadda a da ake kira Prince’s Trust, ta ƙaddamar da ayyukan ta a Nijeriya, inda ta gabatar da shirye-shiryen da ke da nufin rage rashin aikin yi a tsakanin matasa da tallafa wa harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar nan.

Tags: FadarBuckinghamSarkiCharlesShugabaBolaTinubuziyara
Previous Post

Shettima ya jajanta wa al’ummar Kaiama, ya jaddada ƙudirin Tinubu na dawo da zaman lafiya a faɗin Nijeriya

Next Post

Ministan Abuja, Wike ya kafa gidan rediyo domin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jihar Ribas

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Ministan Abuja, Wike ya kafa gidan rediyo domin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jihar Ribas

Ministan Abuja, Wike ya kafa gidan rediyo domin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jihar Ribas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!