• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Nijeriya ta sake neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 25, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Nijeriya ta sake neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada buƙatar a bai wa Nijeriya kujerar dindindin a Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen da ake son yi wa tsarin majalisar.

Tinubu, wanda mataimakin sa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a zauren tattaunawa na Babban Taron majalisar karo na 80 a birnin New York.

Ya ce: “Ya zama dole Nijeriya ta samu kujerar dindindin a Kwamitin tsaro. Wannan wani muhimmin ɓangare ne na sauye-sauye domin dawo da amincewa ga wannan hukuma, wadda ita ce ginshiƙin tsarin haɗin gwiwa na duniya.”

Shugaban ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya za ta dawo da martabar ta ne kawai idan ta dace da yanayin duniya na yanzu, ba ta bar tarihi ya ɗaure ta ba.

Wakilan Nijeriya suna sauraren Shettima a taron

Ya bayyana cewa lokacin da aka kafa majalisar, Nijeriya ƙasa ce ƙarƙashin mulkin mallaka mai mutane miliyan 20, ba tare da samun wakilci a teburin da ake yanke hukunci kan makomar ta ba.

Ya ce: “Yanzu kuwa, mu ƙasa ce mai ‘yanci, muna da fiye da mutane miliyan 236, kuma an yi hasashen nan da shekaru masu zuwa za mu zama ƙasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya.

“Nijeriya ta daɗe tana zama ginshiƙin tsaro a nahiyar Afrika, kuma abar dogaro a aikin kiyaye zaman lafiya na duniya.”

Tinubu ya bayyana cewa sojojin Nijeriya sun taka rawa a cikin ayyuka 51 daga cikin 60 na kiyaye zaman lafiya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar tun bayan samun ‘yancin kai a 1960.

Ya da cewa ƙasar ba ta tsaya ga kan ta ba wajen yaƙar ta’addanci, inda ta yi aiki tare da maƙwabta ƙasashen Afrika ta hanyar Multinational Joint Task Force (MNJTF).

Tinubu ya ce Nijeriya ta koyi darasi daga doguwar gwagwarmaya da ta yi da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi.

Ya ce dalilin da ya sa Nijeriya take magana kan rikicin Gaza, harin da aka kai Ƙatar da sauran tashe-tashen hankali a yankin shi ne saboda ƙwarewar da ƙasar ta samu daga irin waɗannan rikice-rikice da ba sa ƙarewa inda aka fara su.

Tinubu ya ƙara da cewa Nijeriya tana goyon bayan shirin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya na UN80 Initiative, wanda ya yi kira da a sauya tsarin hukumar domin ya dace da zamani, a kuma kawo ƙarshen maimaita ayyuka da ɓata kuɗi.

Tags: Kashim Shettimakujerar dindindinKwamitin TsaroMajalisar Ɗinkin DuniyaNijeriyaShugaba Bola Ahmed TinubuUNGA
Previous Post

Jami’an KAROTA sun kama kayan sola da kwamfutoci na naira miliyan 80 da ɓarayi suka sace a Kano

Next Post

Nijeriya na so a yafe wa ƙasashen da ake bi bashi tare da ba su damar yin kasuwanci domin samun cigaba mai ɗorewa

Related Posts

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Ƙasashen Duniya

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

April 17, 2026
Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta
Ƙasashen Duniya

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

April 3, 2026
Next Post
Nijeriya na so a yafe wa ƙasashen da ake bi bashi tare da ba su damar yin kasuwanci domin samun cigaba mai ɗorewa

Nijeriya na so a yafe wa ƙasashen da ake bi bashi tare da ba su damar yin kasuwanci domin samun cigaba mai ɗorewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!