Jami’an sintiri na Hukumar Kula da Ababen Hawa wato KAROTA, sun kama kayan wuta na sola da suka haura naira miliyan 80, waɗanda da wasu ɓarayi suka sace a yankin Fagge, cikin birnin Kano.
Kakakin Yaɗa Labarai na KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharaɗa, ya ce wasu jami’an sintiri na hukumar ce suka samu nasarar cafke ɓarayin da suka kutsa cikin ɗakin ICT na makarantar sakandare ta gwamnati, wato Aisha Shehu Government Junior Secondary School, Kuka da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.
Da take bayani, Shugabar Makarantar Hajiya Rufa’atu Mahmud Baffa ta ce ɓarayin sun shiga ɗakin ne ta hanyar cire fale-falen rufin ɗakin da kuma farantan sola, inda suka kwashe dukkan kwamfutoci da sauran kayan aikin ICT.
Sai dai sa’a ta kuɓuce wa ɓarayin ne bayan da jami’an KAROTA suka gano kayan a lokacin sintiri, wanda hakan ya tilasta ɓarayin su ajiye kayan suka tsere da gudu.
Da yake tsokaci game da lamarin, Shugaban KAROTA, Faisal Mahmud Kabir ya ce duk da cewa jami’an sa sun bi sahun ɓarayin, ba su samu damar kama su ba, amma duk kayan da suka sace sun bar su, kuma an ƙwato su duka.
Ya kuma ya jinjina wa jami’an sa tare da ƙara masu ƙwarin gwiwa.
Kayan ICT ɗin dai an girke su ne a ƙarƙashin shirin AGILE da Bankin Duniya ke ɗaukar nauyi domin tallafa wa ƙoƙarin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na farfaɗo da harkar ilimi a jihar.
Shugaban KAROTA ya buƙaci gwamnatin jihar da ta ƙara tsaurara tsaro a makarantun da aka girke irin waɗannan kayayyakin domin amfanin ɗalibai.
Rahotanni sun ce ɓarayin sun ɗaure masu gadin makarantar kafin su aikata wannan ta’asa.
Shugaban KAROTA ya tabbatar da cewa an miƙa dukkan kayan da aka ƙwato ga hukumomin makarantar.







