• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Nijeriya na so a yafe wa ƙasashen da ake bi bashi tare da ba su damar yin kasuwanci domin samun cigaba mai ɗorewa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 25, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Nijeriya na so a yafe wa ƙasashen da ake bi bashi tare da ba su damar yin kasuwanci domin samun cigaba mai ɗorewa
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana gabatar da jawabin Nijeriya a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana gabatar da jawabin Nijeriya a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƙasashen duniya da su yafe bashi ga ƙasashe masu tasowa, yana mai cewa hakan hanya ce madaidaiciya ta wanzar da zaman lafiya da cigaba.

Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabin Nijeriya a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana gabatar da jawabin Nijeriya a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.

Ya ce: “Muna buƙatar wani sabon tsarin doka mai ɗorewa, makamancin Kotun duniya ta Kuɗi, wanda zai ba ƙasashe masu tasowa damar kuɓuta daga ɗaurewar tattalin arziki na dogaro da fitar da albarkatun kasa ba tare da sarrafawa ba.”

Tinubu ya bayyana “Lagos Action Plan” da aka tsara shekaru da dama da suka gabata, wadda ta bayyana hanyar kauce wa bashi da dogaro da shi, tare da bai wa ƙasashe damar ƙirƙira daga cikin gida a fannoni kamar noma, ma’adinai da kuma sarrafa man fetur.

Shugaban ya yaba da ƙirƙirar “African Continental Free Trade Area” (AfCFTA), yana mai cewa hakan babban abin alfahari ne da zai ƙara haɗa kan ƙasashen nahiyar.

Ya kuma ce Nijeriya ta tsaya tsayin daka wajen cimma Manufofin Cigaba masu Ɗorewa (SDGs) waɗanda, a cewar sa, za a iya cimma hakan ne ta hanyar maida hankali kan manyan manufofi na haɓakar tattalin arziki da bunƙasa arziki.

Wasu wakilan Nijeriya a taron

Dangane da harkokin Afrika, Tinubu ya ce Nijeriya tana maraba da yunƙurin zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokiraɗiyyar Kwango, tare da jaddada cewa zuba jari na ƙasa da ƙasa zai iya kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka shafi ma’adinai.

Ya ce saka hannun jari a bincike, haɓakawa da kuma sarrafa waɗannan ma’adinai a nahiyar Afrika zai taimaka wajen sauya tsarin samar da kayayyaki ga kasuwar duniya, tare da rage rikice-rikice tsakanin manyan ƙasashe.

Shugaban ya ƙara da cewa Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika sun samu nasarori a cikin shekarun baya-bayan nan wajen gyara harkokin su na cikin gida.

“Idan aka samu sauye-sauye da za su ƙarfafa tsarin kuɗaɗen duniya, za mu iya kai wannan cigaba mataki na gaba, inda kasuwanci, zuba jari da riba za su buɗe sababbin damarmaki ga nahiyar mu,” inji shi.

Tags: bashiKashim ShettimaShugaba Bola Ahmed TinubuUNGAƙasashe masu tasowa
Previous Post

Nijeriya ta sake neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya

Next Post

Ganawa da Guterres: Nijeriya ta jaddada neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya

Related Posts

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Ƙasashen Duniya

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

April 17, 2026
Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta
Ƙasashen Duniya

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

April 3, 2026
Next Post
Ganawa da Guterres: Nijeriya ta jaddada neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya

Ganawa da Guterres: Nijeriya ta jaddada neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!