• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Nijeriya ta ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi da wani Sanatan Amurka ya yi

Wakilin Mu by Wakilin Mu
October 8, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata masu cewa ana yi wa Kiristocin Nijeriya kisan ƙare dangi 
Alhaji Mohammed Idris

Alhaji Mohammed Idris

Gwamnatin Tarayya ta sake ƙaryata zargin da wani Sanatan ƙasar Amurka wai shi Ted Cruz ya yi cewa wai ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya ƙaryata zargin a cikin wata hira ta musamman da Fox News Digital da ke Amurka ta wallafa a ranar Talata.

Ministan ya ce: “Gwamnatin Nijeriya ta ƙi amincewa da wannan zargi. Wannan ba gaskiya ba ne kwata-kwata.”

Yayin da yake mayar da martani kan alƙaluman da Sanata Cruz ya bayar, Idris ya ce: “Ba gaskiya ba ne. Wannan ba shi ne abin da ke faruwa ba. Ina nufin ba gaskiya ba ne a ce an ƙone fiye da coci-coci har 20,000. Kuma ƙarya ce a ce an kashe Kiristoci 52,000. Daga ina ya samo waɗannan alƙaluma? Ba shi da wata hujja ko shaidar da ya dogara da ita. Gwamnatin Nijeriya ta ƙi amincewa da wannan zargi.”

Ya kuma jaddada cewa babu wani jami’in gwamnati ko wata hukuma a Nijeriya da ke mara wa ‘yan ta’adda baya ko yin aiki tare da su don kai hari ga mabiya wani addini.

A cewar sa: “Babu wani jami’in gwamnati a Nijeriya da zai goyi bayan masu tayar da ƙayar baya don su kai hari ga mabiyan wani addini. Wannan zargi ƙarya ne ɗari bisa ɗari.”

Ministan ya sake tabbatar da cewa Nijeriya ƙasa ce mai yawan addinai da kuma zaman lafiya da juna, inda ya ce: “Nijeriya ƙasa ce da ke da mabiya addinai daban-daban. Muna da Kiristoci, muna da Musulmai, har da waɗanda ba sa bin waɗannan addinai biyu. Nijeriya ƙasa ce mai yarda da bambancin addinai. Gwamnatin Nijeriya ta ƙudiri aniyar tabbatar da cewa ana da ‘yancin yin addini a ƙasar nan.”

Ya ƙara da cewa matsalar ta’addanci ta shafi kowa, ba tare da la’akari da addini ba. Ya ce: “Abin baƙin ciki ne cewa waɗannan ‘yan ta’adda suna kashe Kiristoci da Musulmai a wurare daban-daban da suke samun goyon baya. Don haka, ba gaskiya ba ne. Gaba ɗaya ƙarya ce a ce wai ana da wani shiri ko ƙudiri na gangan don hallaka wata ƙungiyar addini; wannan ba daidai ba ne, abin takaici ne ƙwarai.”

Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya tana da cikakken ƙudirin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, inda ya jaddada cewa hukumomin tsaro na ƙasar nan ba su yi ƙasa a gwiwa ba a yaƙi da ta’addanci da fashi da makami a kowane salo.

Tags: Kiristocikisalabarin bogimartaniMohammed Idrisraddita'addanciTed Cruz
Previous Post

CBN ya gindaya sababbin ƙa’idoji da sharuɗɗan amfani da POS

Next Post

Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya mallaki fiye da dala biliyan 1

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya mallaki fiye da dala biliyan 1

Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya mallaki fiye da dala biliyan 1

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!