• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya gindaya sababbin ƙa’idoji da sharuɗɗan amfani da POS

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
October 8, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya gindaya sababbin ƙa’idoji da sharuɗɗan amfani da POS

 

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gindaya sababbin sharuɗɗa da ƙa’idojin amfani da P.O.S a hadahadar kuɗaɗe ta yau da kullum.

Daga cikin sababbin ƙa’idojin, an gindaya cewa ba a yarda ejan masu tiransifa da P.O.S su zarce tiransifa ta sama da Naira miliyan 1 da dubu 200 ba (N1.2m) a duk P.O.S ɗaya a kowace rana.

Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a ranar Talata, ya ce an fito da sababbin sharuɗɗan domin tabbatar da sa-ido da kuma inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe.

Sanarwar wadda Daraktan Kula da Tsare-tsaren Biyan Kuɗaɗe, Musa Jimoh ya sa wa hannu, ya ce hakan zai sa tsarin hada-hadar kuɗaɗe na zamani ya kare kwastomomi sosai daga faɗawa tsilla-tsillar matsalolin yau da kullum da suke fuskanta a tsarin tiransifa ta P.O.S.

Ya ce kuma wajibi ne dukkan bankuna su riƙa bada rahotannin hadahadar kuɗaɗen da ejan-ejan ɗin su suka yi da P.O.S, domin ƙarfafa sa-ido a tsarin hadahadar tare da inganta shi.

Yayin da sanarwar ta fara aiki nan take, ta kuma ƙara da cewa daga 1 ga Afrilu, 2026 za a tabbatar ana bada bayanan daidai wurin da kowane mai P.O.S ke zaune.

“Dukkan bankuna da masu ruwa da tsaki na cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe su tabbatar da cewa ana bin waɗannan sababbin sharuɗɗa waɗanda CBN ya gindaya.”

A ƙarƙashin wannan sabon tsari, tilas ejan ya riƙa hada-hadar kuɗaɗe da P.O.S ta hanyar amfani da asusun banki da ya ware musamman domin hada-hadar ko kuma ‘Asusun Tafi da Gidan Ka’ na ‘wallet’ daga wata cibiyar hada-hadar kuɗaɗe ta zamani, domin tabbatar da samun sauƙin sa-ido da bibiyar abin da ke gudana.

CBN ya yi gargaɗin cewa wanda ya yi amfani da asusun da ba shi aka tantance masa ba, to shi wannan ejan ɗin ya karya ƙa’idar da tilas sai an hukunta shi.

Duk ejan ɗin da aka samu da laifin zamba, rashin bin ƙa’ida, ko wasu laifukan da dokar hada-hadar kuɗi ta haramta, to za a sa-ido a kan sa, kuma a soke yarjejeniyar da aka ƙulla da shi.

An kuma umurci cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe su buga sunayen dukkan ejan-ejan ɗin su a shafin su na intanet, tare da rubuta sunayen dukkan rassan da ejan-ejan ɗin ke ƙarƙashi.

Manyan ejan-ejan, wato ‘Super Ejan’ tilas ya kasance akwai aƙalla ejan guda 50 a ƙarƙashin kowane ‘Babban Ejan’, a faɗin shiyyoyin ƙasar nan shida. Yin hakan zai tabbatar da kowane lungu ya samu damar yin hada-hadar kuɗaɗe ta zamani kuma a sauƙaƙe.

Wasu daga cikin sharuɗɗan kuma sun haɗa da cewa: “An hana ejan mai amfani da na’urar P.O.S sauya wurin zama, matsawa nesa ya yi tiransifa ko rufe wurin hada-hadar sa ba tare da neman izini daga Babban Ejan ba.

“Duk ejan ɗin da zai canja wurin zama, tilas ya manna sanarwar yin haka a wurin da yake hada-hada, tun kwanaki 30 kafin zuwan ranar da zai canja wuri.

An kuma buƙaci cibiyoyi ko kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe su fito da wani tsarin amfani da na’urorin da za su riƙa maida wa kwastoma kuɗaɗen sa, nan take idan aka cire, amma ba su je inda aka tura ba, bayan an rigaya an cire masa.

Tilas a riƙa ajiye rasiɗin aikawa ko cirar kuɗi mai ɗauke da sunan ejan ɗin da shiyyar da yake, har tsawon shekaru biyar.

CBN ya ce an fito da sababbin sharuɗɗan domin inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe, sa-ido tare da tabbatar da jama’a da dama na samun yin hada-hada cikin sauƙi a kowane lungu suke.

Tags: CBNPOS
Previous Post

Tsofaffin ’yan jarida a Kano sun miƙa tsarin kafa ƙungiya ga kwamishina

Next Post

Nijeriya ta ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi da wani Sanatan Amurka ya yi

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata masu cewa ana yi wa Kiristocin Nijeriya kisan ƙare dangi 

Nijeriya ta ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi da wani Sanatan Amurka ya yi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!