• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

ALI KANO by ALI KANO
May 10, 2026
in Siyasa
A A
0
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Alhaji Abdullahi Bello Boɗejo

Alhaji Abdullahi Bello Boɗejo

Jami’an tsaro sun miƙa Alhaji Abdullahi Bello Boɗejo, ɗan takarar kujerar Sanatan Yankin Taraba ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a Abuja.

Bello Boɗejo dai shi ne shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore.

Jami’an tsaro ne suka kama shi a daren Alhamis bayan ya isa Jalingo ta Filin Jirgin Sama na Ɗanbaba Suntai.

A cewar mataimakin sa na musamman, Malam Umar, an kama ɗan takarar na APC ne bayan wasu abokan siyasar sa sun raka shi zuwa ofishin wata hukumar tsaro.

Da yake magana ta wayar tarho da jaridar Daily Trust, Umar ya ce an riga an kai Boɗejo Abuja kuma an miƙa shi ga EFCC.

Ya ce har yanzu ba a bayyana wa iyalan sa irin laifin da ake zargin sa da aikatawa ba.

Ya yi zargin cewa kama shi ya samo asali ne daga yadda farin jinin sa yake ƙaruwa a tseren neman kujerar Sanatan Taraba ta Tsakiya.

Ya kuma zargi wasu manyan jami’an gwamnati da ’yan siyasa a jihar da kitsa kama shi.

“Yayin da nake magana da kai yanzu, ana dab da kammala tantance ’yan takarar gwamna, na Majalisar Dattawa da ta Wakilai, kuma manufar waɗanda suka kitsa kama shi ita ce su hana shi shiga aikin tantancewar,” inji Umar.

Tags: APCBello BoɗejokamusanatatakaraTaraba
Previous Post

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

Next Post

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

Related Posts

Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano
Siyasa

Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano

May 5, 2026
Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci
Siyasa

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

April 28, 2026
Next Post
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!