• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

* JAMB za ta sanya makin yanke UTME na 2026 a yau

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
May 11, 2026
in Ilimi
A A
0
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Wasu ɗaliban makarantar sakandare

Wasu ɗaliban makarantar sakandare

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sababbin tsauraran matakai da nufin yaƙi da shaye-shayen muggan ƙwayoyi da sauran abubuwan maye a makarantun sakandare, ciki har da tilasta gwajin ƙwayoyi ga ɗalibai da kuma dakatar da waɗanda aka ci gaba da samun suna ɗauke da ƙwayoyi a jinin su bayan sun bi hanyoyin jinya da gyaran hali.

An bayyana waɗannan matakai ne a cikin daftarin “Jagororin Ƙasa na Aiwatar da Matakan Yaƙi da Amfani da Ƙwayoyi da Abubuwan Maye a Makarantun Nijeriya” na makarantun sakandare.

Bisa ga jagororin, duk sababbin ɗaliban da aka karɓa a makarantun sakandare za a yi masu gwajin ɗin tilas don tantance amfani da ƙwayoyi tun daga lokacin shigar su makaranta.

Takardar ta bayyana cikakken tsarin da aka tsara domin rage yawaitar shaye-shaye tsakanin ɗalibai da samar da yanayin koyo mai aminci a makarantu a faɗin ƙasar nan.

A cewar takardar manufofin, manufar shirin ita ce “ƙirƙirar yanayi mai dacewa da koyarwa da koyo a cibiyoyin ilimi ta hanyar rage mummunan tasirin da shaye-shaye yake yi ga lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma nasarar karatun ɗalibai.”

Jagororin sun kuma ce, “Za a yi wa duk sababbin ɗalibai gwajin ƙwayoyi da sauran matakan da makarantu ko cibiyoyin koyo suka amince da su tun daga lokacin shiga,” tare da ƙarawa da cewa dole ne a gudanar da hakan “tare da haɗin gwiwar cibiyoyin lafiya na tarayya ko jihohi da aka amince da su da kuma bin hanyoyin da suka dace.”

Baya ga gwajin shiga kafin makaranta, ana sa ran makarantu za su riƙa gudanar da gwaje-gwajen ƙwayoyi lokaci-lokaci da kuma na bazata ga sababbi da tsofaffin ɗalibai aƙalla sau ɗaya a kowane zangon karatu.

Takardar ta ce, “Duk ɗalibai za su riƙa yin gwajin ƙwayoyi lokaci-lokaci kamar yadda hukumomin da suka dace suka ba da shawara.”

Haka kuma, an hana ɗalibai amfani ko mallakar muggan ƙwayoyin narcotic, ƙwayoyin da ake sarrafawa, ko sauran abubuwan maye ba tare da izinin hukumomin makaranta ba.

“An haramta wa duk ɗalibai amfani ko kasancewa da muggan ƙwayoyin narcotic, ƙwayoyin da ake sarrafawa ko abubuwan maye ba tare da amincewar hukumar makaranta ba,” inji jagorar.

Sai dai manufar ta bayyana cewa ɗaliban da ke buƙatar wasu magunguna na musamman saboda rashin lafiya dole ne iyayen su ko masu kula da su su bayyana hakan yayin neman shigar su makaranta.

Sabon tsarin ya kafa matakai uku na gwaji da tsoma baki ga ɗaliban da aka samu suna amfani da ƙwayoyi.

A cewar takardar, “Manufar ita ce a gano ɗaliban da ke buƙatar taimako da kuma inganta yanayin makaranta mai lafiya da aminci.”

Ɗaliban da suka faɗi a gwajin farko za a ba su shawarwari da jinyar farko kamar yadda hukumomin makaranta suka ga dama.

Takardar ta bayyana cewa, “Mutanen da aka samu suna ɗauke da ƙwayoyi za su bi matakan farko na tsoma baki da jinya, ciki har da ba da shawara kamar yadda hukumar makaranta ta ga ya dace.”

Waɗanda aka sake samu suna ɗauke da ƙwayoyi a karo na biyu za a tura su ga ƙwararru domin a ba su kulawa ta musamman.

Jagorar ta ƙara da cewa, “Idan aka sake samun ɗalibi ɗauke da ƙwayoyi, hukumar makaranta za ta tura shi ga ƙwararre domin samun magani da kulawar da ta dace.”

Ga ɗaliban da aka ci gaba da samu suna amfani da ƙwayoyi har bayan gwaji da tsoma baki na uku kuwa, manufar ta tanadi yiwuwar dakatar da su na ɗan wani lokaci daga muhallin makaranta.

Ta ce, “Idan aka sake samun ɗalibi ɗauke da ƙwayoyi, za a dakatar da shi daga makaranta na ɗan wani lokaci domin samun jinya daga ƙwararre da kuma gyaran hali kamar yadda ƙwararren ya ga ya dace.”

Manufar ta kuma ƙaddamar da tsarin ba da shawara kafin da bayan gwaji ga ɗaliban da ake tantancewa.

A cewar takardar, “Shawarar kafin gwaji ita ce jagoranci da ake bai wa mutum kafin a yi masa gwajin ƙwayoyi. Manufar ta ita ce a shirya mutum, a bayyana abin da ake tsammani, a rage fargaba, a ƙarfafa haɗin kai da gina amincewa.”

Ta ƙara da cewa, “Shawarar bayan gwaji tana faruwa bayan sakamako ya fito, ko sakamakon ya nuna akwai ƙwayoyi ko babu. Manufar ita ce a taimaka wa mutum ya karɓi sakamakon tare da haɗa shi da taimakon da ya dace.”

Domin tabbatar da bin doka, ana sa ran kowace makaranta ta kafa kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin shugaban makaranta tare da fayyace aikin sa.

Jagorar ta kuma umurci cewa duk wani tashin hankali da ke da alaƙa da shaye-shaye, ciki har da faɗa ko jikkata wasu, “dole ne a kai rahoto ga jami’an tsaro.”

Haka kuma ta yi gargaɗin cewa ɗaliban da suka ƙi bin tsarin jinya ko gyaran hali za a ware su na ɗan lokaci daga makaranta “har sai an tabbatar sun daidaita.”

Wannan lamarin ya zo ne yayin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar shaye-shaye tsakanin matasa a Nijeriya, inda masu ruwa da tsaki a fagagen ilimi da kiwon lafiya suke gargaɗi kan tasirin sa ga karatu, ladabi, lafiyar ƙwaƙwalwa da tsaron makarantu.

Yayin da masu goyon baya suke ganin matakan za su taimaka a rage shaye-shaye tsakanin ɗalibai, ana sa ran masu suka za su nuna damuwa kan yadda za a aiwatar da su, kariyar jin daɗin ɗalibai, da kuma shirye-shiryen makarantu da cibiyoyin lafiya wajen aiwatar da manufar a faɗin ƙasar nan.

A wani ɓangaren kuma, Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta ba da sanarwar cewa za ta gudanar da Taron Manufofi na 2026 a yau Litinin, inda za a yanke muhimman shawarwari kan shigar ɗalibai manyan makarantu a Nijeriya, ciki har da amincewa da mafi ƙarancin makin shiga makaranta na shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa da mai ba hukumar shawara kan hulɗa da jama’a, Fabian Benjamin, ya fitar ranar Lahadi, hukumar ta ce Ministan Ilimi ne zai jagoranci taron, tare da haɗa masu ruwa da tsaki a fannin ilimi domin tantance “jagororin shigar ɗalibai na 2026 a dukkan manyan makarantu a Nijeriya.”

A cewar sanarwar, taron zai kuma duba tare da amincewa da ma’aunin shiga, ciki har da abin da ta kira “ƙayyade mafi ƙarancin makin da za a iya amincewa da su wajen shiga makarantu,” waɗanda a al’ada ke jagorantar shiga jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi.

Hukumar ta kuma bayyana cewa taron manufofin na 2026 zai karɓi baƙi daga Saliyo, ciki har da Mataimakin Ministan Ilimi na ƙasar, Sarjoh Aziz Kamara, tare da shugabannin jami’o’i biyu — Edwin Momoh na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Ernest Bai Koroma da Bashiru Koroma na Jami’ar Njala.

A cewar sanarwar, jami’an Saliyo sun zo Nijeriya ne domin “nazarin tsarin shigar ɗalibai na tsakiya na ƙasar” yayin da ƙasar su ke duba yiwuwar kafa irin wannan hukuma domin inganta nata tsarin shiga manyan makarantu.

Tun da farko, an yi masu bayani kan hanyoyin jarrabawa da shigar ɗalibai na JAMB a hedikwatar hukumar da ke Bwari, Abuja.

A yayin taron manufofin, ana kuma sa ran baƙin za su ga yadda ake haɗa masu ruwa da tsaki a tsarin shigar ɗalibai na Nijeriya, wanda hukumar ta bayyana a matsayin tsari mai haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori da dama.

Rahotanni sun ce tawagar baƙin ta nuna godiya ga JAMB, tana mai cewa ƙaruwar buƙatar shiga manyan makarantu a Saliyo ta haifar da manyan ƙalubale, yayin da tsarin Nijeriya “yake bayar da mafita mai amfani ga matsalolin da suka daɗe suna neman warakar su.”

Da take jaddada rawar ta a fannin ilimi, sanarwar ta ƙara da cewa tsarin shigar ɗalibai da JAMB take kulawa da shi har yanzu shi ne ginshiƙi wajen rarraba guraben manyan makarantu a Nijeriya, tana mai nuni da cewa masu sukar wanzuwar ta “za su fi fahimtar muhimmancin ta ta dabaru” idan babu ita.

Tags: gwajiJAMBkwayoyisakandareSaliyoUTME
Previous Post

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

Next Post

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta fara horas da matasa 260,000 a fannoni daban-daban na sana’o’in dogaro da kai
Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa kiran kan su ‘Dakta’

May 6, 2026
Ku daina kira na Bahaushe, cewar Bishop Kukah ga ’yan Nijeriya
Ilimi

Ku daina kira na Bahaushe, cewar Bishop Kukah ga ’yan Nijeriya

April 26, 2026
NELFUND ta biya wa ɗalibai 6,385 na Jami’ar Lafiya kuɗin makaranta naira miliyan 795
Ilimi

NELFUND ta biya wa ɗalibai 6,385 na Jami’ar Lafiya kuɗin makaranta naira miliyan 795

April 19, 2026
Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi
Ilimi

Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi

March 15, 2026
Gwamnatin Tarayya ta fara horas da matasa 260,000 a fannoni daban-daban na sana’o’in dogaro da kai
Ilimi

Gwamnatin Tinubu ta buɗe shafin ɗaukar ma’aikatan koyar da sana’o’i a Kwalejojin Fasaha

February 18, 2026
Gyaran tsarin ilimi na Tinubu yana samar da damarmaki ga matasan Nijeriya – Minista
Ilimi

Gyaran tsarin ilimi na Tinubu yana samar da damarmaki ga matasan Nijeriya – Minista

January 24, 2026
Next Post
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!