Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a yau Laraba ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Alhaji Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari.
Mai Shari’a James Omotosho ne ya yanke masa hukuncin a yau Laraba duk da yake bai halarci zaman kotun ba inda aka yi masa shari’a kan ƙarar zargin almundahanar kuɗi da zamba ta naira biliyan 33.8 da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar.
Kotun ta samu tsohon ministan da laifi a duk tuhume-tuhume 12 da EFCC ta shigar a kan sa, inda ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da shari’ar su ba tare da wata shakka mai ma’ana ba.
Mai Shari’a Omotosho ya umurci cewa hukuncin ɗaurin zai gudana a jere, ba a lokaci guda ba, wanda ya kai jimillar shekaru 75 a gidan yari.
Alƙalin ya yanke wa Saleh Mamman hukuncin ɗaurin shekaru bakwai-bakwai a kan tuhume-tuhume na 1, 2, 3, 6, 7, 8, 9, 10, 11 da 12 ba tare da zaɓin tara ba.
Haka kuma, ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru uku a tuhuma ta huɗu tare da zaɓin biyan tarar naira miliyan 10, sannan shekaru biyu a tuhuma ta biyar ba tare da zaɓin tara ba.
Alƙalin ya ce rashin halartar Saleh Mamman a kotu yayin yanke hukunci da zartar da hukuncin wata dabara ce ta ganganci domin hana gudanar da adalci yadda ya kamata.
Bisa tanade-tanaden Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta 2015, kotun ta amince da hujjar lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), cewa za a iya ci gaba da zartar da hukunci duk da rashin halartar wanda ake tuhuma.
Shi dai Saleh Mamman, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa shi Ministan Wutar Lantarki a ranar 21 ga Agusta, 2019. A ranar 1 ga Satumba, 2021 kuma Buhari ya sallame shi daga muƙamin sa, ya maye gurbin sa da Ƙaramin Ministan Ayyuka da Gidaje, Abubakar Aliyu.







