• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotu ta sa a tsare lauya da wasu mutum 4 a kurkuku saboda yi wa Sanatan Bauchi ɓatanci a TikTok

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
October 30, 2025
in Labarai
A A
0
Kotu ta sa a tsare lauya da wasu mutum 4 a kurkuku saboda yi wa Sanatan Bauchi ɓatanci a TikTok
Sanata Shehu Buba Umar, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Ƙasa da Rahotannin Sirri

Sanata Shehu Buba Umar, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Ƙasa da Rahotannin Sirri

Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba ‘yan sanda umurnin a tsare wani lauya mai suna Ahmed Abdulrahman da wasu mutum huɗu a gidan yari saboda ana tuhumar su da yin ɓatanci a intanet da ƙage tare da ƙoƙarin zamba kan wani sanata.

Mai Shari’a Rita Ofili-Ajumogobia ce bada umurnin a yau Alhamis bayan Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda (IGP) ya gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban ta da manyan laifuffuka har 11.

Sauran waɗanda ake zargin su ne Daure David, Ishaq Abubakar Muhammed, Abdulrashid Abdullahi Musa, da Nasiru Usman Abubakar.

A cewar mai gabatar da ƙara, mutanen su biyar sun haɗu suna cin zarafin Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar, Ciyaman na Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Ƙasa da Rahotannin Sirri.

Ana zargin su da wallafa kalaman ɓatanci, bibiya a intanet, da kuma ƙoƙarin zambatar kuɗi daga gare shi.

Waɗanda ake zargin ba su amsa laifin su ba, wanda hakan ya sa lauya mai gabatar da ƙara, Victor Okoye, ya buƙaci kotun da ta tsare su a Gidan Gyara Hali na Kuje har zuwa lokacin da za a fara sauraren ƙarar.

Sai dai lauyoyin su, bisa jagorancin Afeez Matanmi, ya buƙaci kotun da ta ba su beli, musamman wanda ake zargi na farko, Abdulrahman, wanda ya ce lauya ne da bai da niyyar gudu ko ɓata binciken da ake yi.

Ya ce da man ‘yan sanda sun riga sun ba shi beli kafin a zo kotu, kuma bai saɓa ƙa’idojin ba.

To sai dai Okoye ya ƙi yarda da wannan roƙon, ya ce waɗanda ake tuhumar ba su daina yi wa sanatan ɓatanci a intanet ba bayan an ba su belin farkon.

Ya ce: “Wanda ake zargi na farkon yana da hannu dumu-dumu a tuhuma biyar cikin sha-ɗayan da ake yi kuma ya ci gaba da wallafa ɓatanci bayan an ba shi beli. Sana’ar sa ba ta ba shi kariyar ɗaukar laifi ba.”

Ya ƙara da cewa babu dokar da ta tanadi bada damar musamman ga lauyoyi da ake zargi da aikata manyan laifuffuka.

Bayan ta gama sauraren ɓangarorin biyu, sai Mai Shari’a Ofili-Ajumogobia ta bada umurnin cewa Sashen C.I.D. da ke Area 10, Abuja, ta tsare waɗanda ake zargin har zuwa ranar 10 ga Nuwamba.

Ta umurci lauyan Abdulrahman da ya kawo sabuwar takardar amsa ga ƙin da masu ƙara suka yi na ba shi beli kafin ranar da za a koma kotu, lokacin da kotun za ta yanke hukunci kan ita takardar.

Daga nan ta ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 10 ga Nuwamba, 2025.

A Zargi na Ɗaya, an zargi waɗanda aka gurfanar da haɗa kai a cikin shekarar 2025 suna aikata laifin bibiyar sanatan a intanet, wanda hakan laifi ne da ya saɓa wa Sashe na 27(1)(b) na Dokar Laifukan Intanet (Cybercrimes Act) (mai gyara).

A Tuhuma ta Uku, an zargi Abdulrahman da yaɗa wani bidiyo a TikTok (“Kibanna Channel”) da YouTube inda ya yi ƙaryar cewa Sanata Umar yana da hannu wajen ɗaukar nauyin ‘yan bindiga, da nufin tada hankalin jama’a tare da jefa sanatan cikin fargabar za a kashe shi.

Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da ƙoƙarin ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar, wato Daure David, da ƙoƙarin karɓar naira miliyan 5 daga hannun sanatan bisa burgar cewa wai zai hana wata zanga-zanga da ake so a shirya a kan sanatan.

Tags: Barrister Ahmed Abdulrahmankotulaifin intanetMai Shari'a Rita Ofili-AjumogobiaSanata Shehu Buba Umartuhumazargi
Previous Post

Farashin abinci yana ƙara sauƙi a yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki

Next Post

Gwamnatin Tinubu ta musanta iƙirarin Shugaban Amurka wai ana tauye haƙƙin Kiristoci da karkashe su a Nijeriya

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gwamnatin Tinubu ta musanta iƙirarin Shugaban Amurka wai ana tauye haƙƙin Kiristoci da karkashe su a Nijeriya

Gwamnatin Tinubu ta musanta iƙirarin Shugaban Amurka wai ana tauye haƙƙin Kiristoci da karkashe su a Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!