• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Farashin abinci yana ƙara sauƙi a yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki

Wakilin Mu by Wakilin Mu
October 29, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Farashin abinci yana ƙara sauƙi a yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki
Kayan abinci a wata kasuwa a Nijeriya

Kayan abinci a wata kasuwa a Nijeriya

Rahotanni daga jihohin Arewa-maso-yamma na nuna cewa farashin kayan abinci ya fara raguwa a kasuwanni sakamakon girbin damina mai albarka da manoma suka samu a bana.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba da aiwatar da manufofin tallafa wa harkar noma da kuma tabbatar da wadatar abinci a ƙasar nan.

A jihohin Kaduna, Kano da Katsina, manoma sun tabbatar da cewa an samu kyakkyawan girbi na hatsi, tumatur, dawa, gero da shinkafa, abin da ya janyo farashin kayan abinci ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Misali, a kasuwannin Kaduna buhun shinkafa na kilo 50 da ake sayarwa a kan N100,000 a baya, yanzu ya koma tsakanin N50,000 zuwa N63,000, haka kuma farashin kwandon tumatur ya sauka daga N120,000 zuwa N35,000.

Wani ɗan kasuwa a Dawanau, Kano, Alhaji Bala Ali, ya tabbatar da cewa “yawan amfanin gona daga ƙauyuka ya ƙaru sosai, abin da ya taimaka wajen daidaita farashin abinci da kuma tabbatar da wadatar kayan masarufi a kasuwa.”

A Jihar Kano, rahotanni sun ce yawancin manoma sun samu gagarumin girbi saboda yanayin ruwan sama da ya yi daidai da lokacin noma.

Wasu manoma ma sun yaba da shirin “Special Agro-Industrial Processing Zone” (SAPZ) da suka ce ya taimaka wajen samun iri da dabarun noma na zamani.

Wani manomi a Bebeji, Malam Audu Muzammil, ya ce, “Ruwan sama ya yi wadata kuma kwari sun yi ƙasa matuƙa. Daman abin da ya rage mana shi ne adana kayan mu yadda ya kamata. Amma girbi ya yi albarka sosai.”

A Jihar Katsina kuwa, duk da cewa wasu manoma sun koka da tsadar takin zamani, suna murna da cewa farashin kayan abinci ya ragu, abin da ya sa mutane da dama ke iya sayen abinci cikin sauƙi.

Malam Kabir Sabi’u, wani manomi daga Katsina, ya ce, “Duk da cewa mun yi asara saboda farashi ya fadi, muna gode wa Allah saboda jama’a da dama yanzu suna iya siyan abinci cikin rahusa. Wannan ma wata ni’ima ce.”

Masana tattalin arziki na cewa wannan sauƙin farashin abinci alama ce ta daidaituwar kasuwa da kuma nasarar da ake samu daga manufofin gwamnati na inganta noma, samar da kayan aikin gona da kuma rage dogaro da abinci daga ƙasashen waje.

Gwamnatin Tarayya dai ta bayyana cewa za ta ci gaba da tallafa wa manoma ta hanyar samar da kayayyakin ajiyar amfanin gona, rarraba iri da takin zamani a farashi mai rahusa da kuma inganta tsaro a yankunan karkara domin ƙarfafa noman cikin gida.

Da dama daga cikin ‘yan ƙasa sun bayyana farin ciki da saukar farashin kayan abinci, musamman bayan dogon lokaci da ake fama da hauhawar farashi.

“Yanzu muna ganin canji a zahiri,” inji wata mata a Kano, Hajiya Fatima Sani.

“Tumatur, shinkafa, wake, duk sun yi sauƙi. Allah ya ƙara albarka ga manoma da gwamnati,” inji ta.

Masu lura da al’amuran tattalin arziki na cewa idan gwamnati ta ci gaba da wannan tsarin, akwai yiwuwar farashin abinci zai ci gaba da daidaituwa kuma hakan zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki ga jama’a.

Tags: farashikasuwakayan abinci
Previous Post

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

Next Post

Kotu ta sa a tsare lauya da wasu mutum 4 a kurkuku saboda yi wa Sanatan Bauchi ɓatanci a TikTok

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Kotu ta sa a tsare lauya da wasu mutum 4 a kurkuku saboda yi wa Sanatan Bauchi ɓatanci a TikTok

Kotu ta sa a tsare lauya da wasu mutum 4 a kurkuku saboda yi wa Sanatan Bauchi ɓatanci a TikTok

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!