Nijeriya da Birtaniya sun rattaba hannu kan manyan yarjejeniyoyi uku da suka shafi haɗin gwiwar harkokin hijira, laifuffukan shige-da-fice na tsari, tsaron iyakoki, da kuma faɗaɗa bizar kasuwanci ga kamfanonin Birtaniya da ke aiki a Nijeriya.
An bayyana yarjejeniyoyin ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar a shafin ta na X a jiya Alhamis, a matsayin wani ɓangare na tattaunawar da ake ci gaba da yi yayin ziyarar aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai Birtaniya.
An ruwaito Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, yana cewa yarjejeniyoyin “suna nuna ƙoƙarin Nijeriya na kafa tsarin hijira mai gaskiya, bisa ƙa’ida, wanda yake da tsaro, tsari mai kyau kuma mai amfani ga ɓangarorin biyu.”
Ya ƙara da cewa za su taimaka wajen magance “cin zarafin hanyoyin doka” tare da ƙarfafa tsaron iyakoki.
Ya kuma bayyana cewa ana sa ran yarjejeniyoyin za su inganta kasuwanci tare da sauƙaƙa zirga-zirgar harkokin kasuwanci, wanda hakan zai tallafa wa manyan manufofin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya.
A cewar sa, shirye-shiryen suna goyon bayan burin Nijeriya na kaiwa tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta hanyar kawar da shingayen da ke da alaƙa da hijira ba bisa ƙa’ida ba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an rattaba hannu kan yarjejeniyoyin tare da Sakatariyar Harkokin Cikin Gida ta Birtaniya, Shabana Mahmood, da wakiliyar kasuwancin Birtaniya, Florence Eshalomi.
Yarjejeniyoyin suna nuna wani muhimmin mataki a dangantakar Nijeriya da Birtaniya, inda suke ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin tafiyar da harkokin hijira, tsaro, da bunƙasar tattalin arziki.
Rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hijira da biza tsakanin Nijeriya da Birtaniya suna zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da wasu yarjejeniyoyi da hulɗoɗi tsakanin ƙasashen biyu yayin ziyarar kwanaki biyu da Tinubu ke yi a Birtaniya.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka fito daga ziyarar shi ne yarjejeniyar samar da kuɗaɗe fam miliyan 746 domin sabunta tashoshin jiragen ruwa na Legas.
Tashar Jiragen Ruwa ta Legas da ke Apapa da kuma tashar Tin Can Island suna da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin teku na Nijeriya, domin su ne manyan ƙofofin shigo da kaya da fitar da su.
Tashoshin suna sarrafa kaso mai yawa na jigilar kaya a ƙasar nan, kuma suna da muhimmanci wajen ayyukan kwastam, samar da kuɗaɗen shiga, da kuma gaba ɗaya harkokin tattalin arziki.







