• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Rikicin ADC ya rincaɓe yayin da shugabannin ta na jihohi 36 suka maka NWC a kotu

* Suna so kotu ta taka wa su David Mark birki

ALI KANO by ALI KANO
March 20, 2026
in Siyasa
A A
0
Rikicin ADC ya rincaɓe yayin da shugabannin ta na jihohi 36 suka maka NWC a kotu
Sanata David Mark, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na ADC

Sanata David Mark, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na ADC

Wani sabon rikicin shugabanci ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC), yayin da shugabannin ta na dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya suka shigar da ƙara a kotu kan Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa zargin take dokokin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga wasu matakai da NWC ɗin, wanda ke ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, ya ɗauka, musamman kafa kwamitoci domin kula da zaɓen fidda gwani na jihohi da aka shirya gudanarwa a watan Afrilu.

Kwamitocin Gudanarwa na Jihohi da abin ya shafa sun zargi shugabannin jam’iyyar na ƙasa da kutsawa cikin ayyukan da kundin tsarin mulki ya tanadar musu, ta hanyar kafa tsare-tsare kai-tsaye don gudanar da zaɓen fidda gwani, suna mai jaddada cewa irin waɗannan ayyuka na hannun kwamitocin zartarwa na jihohi ne kaɗai bisa dokokin jam’iyyar.

A cikin takardar ƙarar da suka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, masu ƙarar suna neman kotu da ta shiga tsakani domin dakatar da shirye-shiryen zaɓen fidda gwanin.

Suna kuma neman umurnin wucin gadi (interlocutory injunction) da zai hana NWC ci gaba da aiwatar da shirin har sai an yanke hukunci kan ƙarar.

Ƙarar ta kuma taso da tambayoyi kan halascin kwamitin riƙon ƙwarya ko na wucin gadi da NWC ya kafa, musamman ko yana da hurumin shirya zaɓen fidda gwani na jihohi.

Haka kuma, masu ƙarar sun ƙalubalanci sahihancin naɗa kwamitocin taro ba tare da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Wani muhimmin batu da ke gaban kotun shi ne wa’adin mulkin kwamitocin zartarwa na jihohi na yanzu. Masu ƙarar sun ce wa’adin su na shekaru huɗu yana nan daram har sai an gudanar da zaɓuɓɓukan taron jihohi da babban taron ƙasa bisa ƙa’idojin kundin tsarin mulki.

An shigar da ƙarar ne ta hannun Don Norma Obinna da wasu mutum shida a madadin shugabannin jihohin.

Waɗanda ake ƙara sun haɗa da ADC, da shugaban NWC David Mark, da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC), da sauran ɓangarori masu ruwa da tsaki.

Daga cikin buƙatun da ake nema akwai umurnin da zai hana tsoma baki cikin ayyuka da wa’adin shugabannin jihohi, tare da ayyana naɗin membobin kwamitin taro da NWC na rikon ƙwarya ko na wucin gadi ya yi a matsayin mara inganci.

Tags: adawaADCDavidMarkkotuzaben2027ƙara
Previous Post

Tinubu ya taya Musulmi murnar Ƙaramar Sallah tare da kira zuwa ga kishin ƙasa

Next Post

Nijeriya da Birtaniya sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi kan hijira, tsaron iyakoki, da bizar kasuwanci

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Nijeriya da Birtaniya sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi kan hijira, tsaron iyakoki, da bizar kasuwanci

Nijeriya da Birtaniya sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi kan hijira, tsaron iyakoki, da bizar kasuwanci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!