A yayin da babban zaɓen 2027 yake ƙara matsowa, Gwamnan Jihar Anambra, Dakta Charles Soludo, ya ce jam’iyyar sa ta All Progressives Grand Alliance (APGA) ba za ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba.
Ya bayyana hakan ne a yau Juma’a lokacin wata tattaunawa da manema labarai a Awka, babban birnin jihar, kwanaki uku bayan an rantsar da shi a karo na biyu.
“Ba za mu tsayar da ɗan takara ba,” in ji tsohon masanin tattalin arziki da ya zama ɗan siyasa, yayin da yake mayar da martani kan shirye-shiryen jam’iyyar sa na zaɓen 2027.
“A shekarar 2011, APGA ba ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba. APGA ta mara wa Shugaba Jonathan baya ne, wanda a lokacin shi ne shugaban ƙasa, a matsayin ɗan takararta,” inji shi.
Jagoran na APGA ya yi alƙawarin goya wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, yana mai cewa jam’iyyar sa yana aiki kafaɗa da kafaɗa tare da Gwamnatin Tarayya.

Da yake bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin abokin sa, gwamnan ya ce tsohon gwamnan na Jihar Legas ya yi aiki mai kyau tun bayan hawan sa mulkin ƙasar nan a 2023.
Ya nemi a mara wa Tinubu baya don wa’adi na biyu, yana mai cewa shi ne zai yi nasara a babban zaɓe mai zuwa.
Soludo ya ce: “Ta fuskar kai na da ta jam’iyya, babu wata shakka. Shugaba Asiwaju Bola Tinubu aboki na ne. Ina ganin ya yi aiki mai kyau kuma ya cancanci wa’adi na biyu. Ba ni da wani uzuri a kan hakan; wannan shi ne matsayi na.
“Amma ban da haka ma, akwai muhimmin abu wanda ya shafi muradun jama’a ta. Batun jama’a ta ne; dole ne su kasance suna da tasiri a teburin yanke shawara. Zai yi nasara ko da APGA ko babu APGA.”
A yayin tattaunawar kai-tsaye da manema labarai, ya kuma yi magana kan matakan da gwamnatin sa ta ɗauka na taƙaita ayyukan bokaye a Jihar Anambra.
Soludo ya bayyana cewa ba ya adawa da addinin gargajiya, amma ya yi gargaɗi cewa wasu masu aikata laifi suna aikata miyagun laifuffuka a ƙarƙashin sunan bauta ta gargajiya.
Gwamnan ya ce wasu bokaye suna da hannu wajen shirya tsafe-tsafe ga masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami, kuma suna aikata munanan ayyuka da ka iya haɗawa da hadayar mutane domin kuɗi da kariya.
Ya ce haƙƙin gwamnatin jiha ne ta dakatar da irin waɗannan al’amuran sihiri da suka haifar da munanan ayyuka da ke sake bayyana cikin sauri a rayuwar al’adu da zamantakewar al’ummar ƙabilar Igbo.

A cewar Soludo, munanan ayyukan irin waɗannan bokaye ba su da alaƙa da ingancin maganin gargajiya ko ayyukan da suka shafi Allah da bil’adama, kuma ya jaddada buƙatar fallasa su da ɗaukar mataki mai tsauri a kan su.







