• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Shettima ya jajanta wa al’ummar Kaiama, ya jaddada ƙudirin Tinubu na dawo da zaman lafiya a faɗin Nijeriya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
February 8, 2026
in Tsaro
A A
0
Shettima ya jajanta wa al’ummar Kaiama, ya jaddada ƙudirin Tinubu na dawo da zaman lafiya a faɗin Nijeriya
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana jajanta wa Sarkin Kaiama, Alhaji Mu'azu Shehu Omar (Kiyaru IV), a lokacin ziyarar 

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana jajanta wa Sarkin Kaiama, Alhaji Mu'azu Shehu Omar (Kiyaru IV), a lokacin ziyarar 

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana jajanta wa Sarkin Kaiama, Alhaji Mu’azu Shehu Omar (Kiyaru IV), a lokacin ziyarar

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci wata tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara domin jajanta wa al’ummar yankin da Gwamnan Jihar, Malam AbdulRahman AbdulRazaq, bisa mummunan harin ta’addanci da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar damuwa a ƙauyukan Nuku da Woro, inda harin ya jefa al’umma cikin alhini da firgici.

A jawabin sa ga jama’a da shugabannin yankin, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajirce wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Shettima a wurin ta’aziyyar a Kaiama
Sarkin Kaiama, Alhaji Mu’azu Shehu Omar (Kiyaru IV), a lokacin ziyarar ta Kashim Shettima

Shettima ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa ya bayar da umurnin tura bataliyar Sojojin Nijeriya zuwa Kaiama domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ƙara da cewa dukkanin hukumomin tsaro suna aiki tare, kuma an ɗauki matakai na musamman domin kawar da barazanar rashin tsaro ba kawai a Kaiama ba, har da faɗin Jihar Kwara baki ɗaya.

Ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai, tare da yin addu’a domin zaman lafiyar yankin.

Dandazon mahalarta taron ta’aziyyar

Gwamnan Jihar Kwara, Malam AbdulRahman AbdulRazaq, ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa gaggawar ɗaukar mataki, yana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen dawo da ƙwarin gwiwa da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Manyan baƙi
Tags: jajeKaiamaKashimShettimaKiyaruIVKwaraMu'azuShehuOmarta'addancita'aziyyatsaro
Previous Post

Za a buɗe kan iyakar Nijeriya da Nijar ta Tsamiya da ke Kebbi don cinikayya

Next Post

Bayan shekaru 37, Tinubu zai kai ziyarar musamman zuwa Birtaniya

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa
Tsaro

’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin garkuwa da mutane, kuma sun ƙwato makamai a Nasarawa

May 8, 2026
Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
Next Post
Bayan shekaru 37, Tinubu zai kai ziyarar musamman zuwa Birtaniya

Bayan shekaru 37, Tinubu zai kai ziyarar musamman zuwa Birtaniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!