Jami’ar Capital City da ke Kano (CCUK) ta naɗa Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, a matsayin Uban Jami’ar (Visitor), matakin da jami’ar ta ce zai ƙara ƙarfafa ƙoƙarin ta na samar da nagartar ilimi, bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ƙarfafa hulɗa da al’umma.
An bayyana wannan naɗi a ne yayin wata ziyarar girmamawa da wata babbar tawaga daga jami’ar ta kai Fadar Sarkin Kano.
Tawagar, wadda ta haɗa da Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT) na jami’ar, da Mataimakin Shugaban Jami’a (Vice-Chancellor) da Magatakardan Jami’a (Registrar), ta miƙa wasiƙar naɗin ga Sarkin.
A cewar jami’ar, wannan naɗi wani muhimmin cigaba ne a tarihin ta, kuma yana nuna irin girmamawa da take yi wa Sarkin bisa gudunmawar da ya daɗe yana bayarwa a fannonin ilimi, hidimar jama’a, bunƙasa tunani da jagoranci a matakin ƙasa.
Jami’ar ta bayyana Sarkin Kano, Sanusi II, a matsayin fitaccen mai rajin ilimi, cigaban al’umma da bunƙasa harkokin ilimi, tana mai cewa jagorancin sa da gogewar sa za su zama abin alfahari da jagora ga jami’ar yayin da take ƙoƙarin ƙarfafa matsayin ta a matsayin cibiyar nagartar ilimi.
Da suke magana yayin miƙa wasiƙar, membobin tawagar jami’ar sun bayyana amannar su da cewa naɗin Sarkin a matsayin Uban Jami’a zai taimaka wajen ciyar da hangen nesan jami’ar gaba, musamman wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, gina kyawawan ɗabi’u da samar da ingantaccen ilimi.
Suka ƙara da cewa alaƙar da jami’ar za ta yi da Sarkin za ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin ilimi, cibiyoyin gargajiya da sauran al’umma baki ɗaya.
“Tabbas wannan naɗi ba wai girmamawa kaɗai ba ne, har ma wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’a, cibiyoyin gargajiya da al’umma gaba ɗaya,” inji tawagar.
Jami’ar ta sake jaddada aniyar ta ta ci gaba da rainon shugabannin gobe ta hanyar samar da ingantacciyar koyarwa, bincike da ayyukan hidima ga al’umma, tare da cin gajiyar hikima da gogewar fitattun mutane masu aƙida da manufofi irin nata.
Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Jami’ar Capital City ya ce jami’ar tana ci gaba da mayar da hankali wajen gina al’adar nagarta da kuma amfani da haɗin gwiwa na dabaru domin cimma burin ta na dogon lokaci.






