Iyalai, abokai da abokan aiki suna cikin jimami bayan rasuwar wata lauya mai shekaru 26, Sarah Araba Tettey, wadda rahotanni suka ce ta kamu da bugun zuciya yayin da take murnar nasarar da ƙasar Ghana ta samu a kan Panama a ranar Laraba.
Tettey, wadda ta kammala karatu a Tsangayar Shari’a ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah (KNUST) da ke Ghana, ta shiga ƙungiyar lauyoyin Ghana a farkon wannan shekarar, kuma ta fara aiki a kamfanin lauyoyi na O & A Legal Consult.
Majiyoyi masu kusanci da lamarin sun bayyana cewa Sarah Araba Tettey tana kallon wasan tare da abokan ta a Standard Hostel, wani masauki mai zaman kan sa da ke Bomso kusa da KNUST, lokacin da lamarin ya faru.
Shaidu sun ce ta faɗi ba zato ba tsammani yayin da ake murnar nasarar Ghana.
Abokai da sauran mutanen da ke wurin suka garzaya da ita zuwa Asibitin KNUST, wanda aka fi sani da Tech Hospital, inda ma’aikatan lafiya suka yi ƙoƙarin farfaɗo da ita ta hanyar amfani da dabarar farfaɗo da bugun zuciya da numfashi (CPR) na kusan mintuna 45.
Sai dai duk da ƙoƙarin da likitoci da ma’aikatan jinya suka yi, daga bisani aka tabbatar da rasuwar ta.
Labarin rasuwar ta ya girgiza lauyoyi a Ghana, musamman ɗalibai da waɗanda suka kammala karatun shari’a a KNUST da kuma abokan karatun ta a Makarantar Shari’a ta Ghana, inda da dama daga cikin su suka san ta kai-tsaye.
Mariganyiyar, wadda abokai da abokan aiki suka fi sani da Araba Tettey, an san ta da ƙwarewa da jajircewa a aikin ta, kuma ana kallon ta a matsayin ɗaya daga cikin matasan lauyoyi masu hazaƙa da ake sa ran za su yi fice a nan gaba.
Rasuwar ta ta jefa mutane da dama cikin alhini, inda suka bayyana ta a matsayin babban rashi na wata haziƙar lauya mai kyakkyawar makoma.
An ajiye gawar ta a mutuware na Makarantar Kiwon Lafiya ta KNUST, yayin da ake jiran ƙarin shirye-shiryen jana’izar ta.
Har yanzu iyalan ta ko hukumomin lafiya ba su fitar da wata sanarwa game da ainihin dalilan rasuwar ta ba.







