Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Jihar Neja (NSUBEB) ta bayyana cewa ta kammala ayyukan gyare-gyare da inganta wasu makarantun firamare a sassan jihar, yayin da ayyukan wasu makarantun ke gab da kammalawa.
Hukumar ta ce an kammala ayyukan gyaran makarantu a ƙananan hukumomin Lapai, New Bussa da Kontagora, yayin da makamantan ayyukan da ake gudanarwa a Gurara, Agaie, Bida da Bokani suka kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammalawa.
Shugaban hukumar NSUBEB, Dakta Liman Ibrahim Alhaji, shi ne ya bayyana hakan a cikin wani rahoto da ya gabatar kan yadda ayyukan ke gudana.
Ya kuma ce aikin gyaran Makarantar Firamare ta Marafa yana ci gaba da tafiya yadda aka tsara.
A cewar sa, cigaban da aka samu wajen gudanar da ayyukan ya samo asali ne daga ƙudirin Gwamnan Jihar Neja na bunƙasa harkokin ilimi, da kuma cikakken goyon bayan da gwamnatin jihar ke bai wa hukumar.
Dakta Liman ya ce hukumar za ta gudanar da rangadi tsakanin ranakun 7 zuwa 10 ga Satumba, 2026, domin duba yadda ayyukan ke gudana a wurare daban-daban tare da membobin hukumar da ƙwararru.
Haka kuma, hukumar ta ce za ta fara bayar da takardun kwangila ga kamfanonin da suka samu ayyukan hukumar daga ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026.
Bayanin ya ce wannan mataki yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Neja take ƙara mayar da hankali kan farfaɗo da ababen more rayuwa a makarantu, domin samar da ingantaccen yanayi na koyo da koyarwa.
A wani ɓangare na bayanin, shugaban na NSUBEB ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga Gwamnan Jihar Neja bisa rasuwar Hon. Aminu Wushishi.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa, ya jiƙan sa da rahama, tare da bai wa iyalan sa, gwamnatin jihar da al’ummar Jihar Neja haƙurin jure wannan babban rashi.






