• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

Raɗɗa ya ƙara tallafin karatun ɗalibai da kashi 100% bayan shekaru 18 ba tare da ƙari ba

UMAR GARBA by UMAR GARBA
October 12, 2026
in Ilimi
A A
0
Raɗɗa ya ƙara tallafin karatun ɗalibai da kashi 100% bayan shekaru 18 ba tare da ƙari ba
Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa yana jawabi a taron ƙaddamar da rabon kuɗaɗen tallafin karatu na Naira miliyan 689.79 ga ɗalibai 19,318 wanda aka gudanar a Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina, Katsina 

Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa yana jawabi a taron ƙaddamar da rabon kuɗaɗen tallafin karatu na Naira miliyan 689.79 ga ɗalibai 19,318 wanda aka gudanar a Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina, Katsina 

Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana ƙarin kashi 100 cikin 100 na kuɗin tallafin karatu da ake bai wa ɗalibai, lamarin da ya kawo ƙarshen shekaru 18 ba tare da an ƙara kuɗin tallafin ba. Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin sa na rage nauyin kuɗi da ke kan ɗalibai da iyayen su.

Gwamnan ya bayyana wannan mataki ne yayin ƙaddamar da rabon kuɗaɗen tallafin karatu na Naira miliyan 689.79 ga ɗalibai 19,318 da aka tantance daga manyan makarantu 97, domin zangon karatu na shekarar 2025/2026.

A wajen taron da aka gudanar a Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina, Radda ya bayyana cewa gwamnatin sa ta raba Naira miliyan 689.79 ga ɗalibai 19,318 da aka tantance daga makarantu 97, domin zangon karatu na shekarar 2025/2026.

Gwamnan ya ce ƙarin kuɗin tallafin ya nuna ƙudirin gwamnatin sa na bai wa ilimi fifiko, faɗaɗa damar samun cigaba da kuma tabbatar da cewa ƙarancin kuɗi bai hana ɗalibai cimma burin su na karatu ba.

Ya ce zuba jari a fannin ilimi yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa mutane, inganta rayuwar iyalai, bunƙasa tattalin arziki da kuma shirya matasa su zama ’yan ƙasa masu bayar da gudunmawa ga cigaban al’umma.

Baya ga ƙarin tallafin karatun ga ɗalibai baki ɗaya, Raɗɗa ya ce gwamnatin jihar ta amince da ƙarin tallafi na musamman ga ɗaliban da ke karatun likitancin dabbobi. Haka kuma, ta ba ɗalibai 56 ’yan asalin Jihar Katsina da ke karatu a Makarantar Shari’a ta Nijeriya tallafin Naira 500,000 ga kowane ɗalibi.

Wasu daga cikin baƙi da suka halarci taron

Ya ƙara da cewa gwamnati tana ci gaba da tallafa wa ɗalibai 118 da ke karatun kwasa-kwasai na musamman a ƙasashen waje.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana ƙaddamar da wani sabon shirin tallafin karatu ga ƙwararrun ɗalibai 1,700 da aka zaɓa daga ƙananan hukumomi 34 na jihar, domin su yi karatu a muhimman fannoni da suka haɗa da aikin jinya, injiniyanci, fasahar sadarwa da bayanai (ICT), aikin gona da kuma ilimi.

A cewar sa, waɗannan shirye-shiryen tallafi daban-daban sun sa jimillar kuɗaɗen tallafin karatu da kyaututtukan da gwamnatin jihar ta bayar ga ɗalibai ta haura Naira biliyan 3.29.

Raɗɗa ya yaba wa Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Katsina bisa ƙoƙarin ta na ƙarfafa gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da shirye-shiryen tallafa wa ɗalibai.

Ya jaddada muhimmancin gano Naira miliyan 86 na kuɗaɗen tallafin karatu da ba a karɓa ba, tare da mayar da su baitulmalin jihar. Ya bayyana wannan mataki a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da kyakkyawan sarrafa dukiyar al’umma.

Gwamnan ya buƙaci ɗalibai da su mai da hankali, su kasance masu ladabi da bin ƙa’ida, tare da jajircewa wajen neman ƙwarewa a karatu. Ya jaddada cewa gwamnatin sa na da burin gina tsarin ilimi da ke ba wa ƙwazo da cancanta lada, inganta daidaiton damar samun ilimi da kuma samar wa matasa ilimi da ƙwarewar da za su taimaka musu wajen ci gaban Jihar Katsina da Nijeriya baki ɗaya.

Ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na ci gaba da zuba jari a fannin ilimi, yana mai cewa makomar jihar ta dogara ne da irin damar ci gaba da aka samar wa matasan ta a yau.

Previous Post

Shettima ga Arewa: Kada ku damu, babu abin tsoro a wa’adin Tinubu na biyu

Next Post

Taron IMF Da Bankin Duniya A Bangkok: Yadda Cardoso ya haskaka wa duniya alfanun zuba jari a Nijeriya don ci gaba mai ɗorewa

Related Posts

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja
Ilimi

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

August 29, 2026
Ilimi

Niger-SUBEB ta tabbatar da ƙarin girma ga malaman da suka cancanta

August 22, 2026
Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris
Ilimi

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

August 20, 2026
Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki
Ilimi

Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

August 4, 2026
Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya
Ilimi

Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ƙulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki a jami’o’i
Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

July 14, 2026
Next Post
Taron IMF Da Bankin Duniya A Bangkok: Yadda Cardoso ya haskaka wa duniya alfanun zuba jari a Nijeriya don ci gaba mai ɗorewa

Taron IMF Da Bankin Duniya A Bangkok: Yadda Cardoso ya haskaka wa duniya alfanun zuba jari a Nijeriya don ci gaba mai ɗorewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!