Wata ƙungiyar al’umma mai suna Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance ta buƙaci Gwamnatin Jihar Kaduna da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Malam Nuhu Ribaɗu, da su gaggauta aiwatar da tsarin nan na Kwance Ɗamara, Rushe Ƙungiyoyin Masu Ɗauke da Makamai da Sake Shigar da Su Cikin Al’umma (Disarmament, Demobilisation and Reintegration – DDR) domin ƙarfafa zaman lafiyar da aka samu a Birnin-Gwari da sauran al’ummomin da ke kewaye da ita.
Ƙungiyar ta bayyana wannan buƙata ne a cikin wata sanarwa da shugaban ta, Ibrahim Abubakar NaGwari, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a yau Asabar.
A cewar ƙungiyar, tsarin DDR yana da muhimmanci matuƙa wajen kare abin da ta kira “Tsarin Zaman Lafiya na Kaduna”, tare da hana komawar yankin cikin matsalar rashin tsaro.
Sanarwar ta ce: “Muna kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro da su fara aiwatar da tsarin Kwance Ɗamara, Rushe Ƙungiyoyin Masu Ɗauke da Makamai da Sake Shigar da Su Cikin Al’umma (DDR) ba tare da ɓata lokaci ba. Wannan yana da matuƙar muhimmanci domin ceto Tsarin Zaman Lafiya na Kaduna daga durƙushewa tare da tabbatar da ɗorewar zaman lafiyar da ake morewa a yanzu.”
Ƙungiyar ta jaddada cewa Birnin-Gwari ta samu gagarumin cigaba a ɓangaren tsaro cikin shekaru biyu da suka gabata, tana mai cewa rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wasu mahajjatan da suka dawo daga aikin Hajjin 2026 a hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna ba gaskiya ba ne, kuma an ƙirƙiro su ne domin kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya.
Ƙungiyar ta ce: “Muna bayyanawa ƙarara cewa babu wani lokaci cikin shekaru biyu da suka gabata da aka samu garkuwa da mutane da yawa a Birnin-Gwari. Iƙirarin cewa an yi garkuwa da wasu mahajjatan da suka dawo daga Hajjin 2026 a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna ƙarya ce da masu adawa da nasarorin zaman lafiya na watanni goma sha takwas da suka gabata suke yaɗawa.”
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin mayar da wasu matsalolin tsaro na daban zuwa batun siyasa, inda ta kawo misalin kisan wani direban mota mai suna Ibrahim Adamu da aka yi kwanan nan.
Duk da yin Allah-wadai da wannan lamari, ƙungiyar ta ce bai kamata irin waɗannan abubuwan da suka faru su rufe idanu kan zaman lafiya da ‘yancin zirga-zirgar da mazauna yankin da matafiya ke morewa a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna ba.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Bai kamata a mayar da matsalolin tsaro makamin neman amfani na siyasa ba.”
Har ila yau, ƙungiyar ta buƙaci hukumomin tsaro da su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da takwarorin su na jihohin Neja, Zamfara da Katsina, tana zargin cewa wasu ɓatagari suna shiga Birnin-Gwari daga waɗannan jihohi domin kawo cikas ga zaman lafiyar da aka samu.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati da ta gaggauta tura jami’an Forest Guards da ake shirin ɗauka zuwa yankunan da ke fama da matsalolin tsaro nan da nan bayan sun kammala horon su, tana mai cewa hakan zai ƙara kare manoma tare da ƙarfafa tsaro a faɗin yankin.
Ta yi kira ga al’ummar Birnin-Gwari da su kasance cikin shiri tare da yin watsi da duk wani yunƙuri daga wasu mutane ko ƙungiyoyi masu son tayar da zaune tsaye da kawo cikas ga zaman lafiya.
Haka kuma, ƙungiyar ta shawarci masu amfani da kafafen sada zumunta da masu tasiri a shafukan sada zumunta da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancin su ba, waɗanda za su iya haifar da firgici tare da kawo cikas ga nasarorin da aka samu a ƙarƙashin Tsarin Zaman Lafiya na Kaduna.
Ƙungiyar ta ce: “Wajibi ne kowa ya bayar da gudunmawar sa wajen kare zaman lafiyar da muka gina tare.”






