Daraktan Gudanarwa na Hukumar Kula da Ilimin Bai Ƙare ta Jihar Neja (Niger-SUBEB), Malam Adamu Isah Lokogoma, ya tabbatar da cewa hukumar za ta tabbatar da gaskiya, adalci da cancanta wajen tantance malaman da za su samu karin girma.
Lokogoma ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga malaman Hukumar Ilimi ta Ƙananan Hukumomi (LGEA) na Suleja da Tafa, yayin da ake gudanar da aikin tantance malaman da suka cancanci karin girma a Suleja.
Ya ce an tsara aikin tantancewar ne domin tabbatar da cewa malaman da suka nuna ƙwazo, jajircewa da ƙwarewa wajen gudanar da aikin su sun samu damar karin girma bisa cancanta.
A cewar sa, karin girma ba wai kawai wata hanya ce ta karrama malamai bisa tsawon shekarun da suka yi suna aiki ba, har ma wata hanya ce ta ƙarfafa gwiwar su da inganta harkar ilimin bai-ɗaya a Jihar Neja.
“Wannan aikin tantancewa muhimmin mataki ne wajen tabbatar da cewa an gane ƙoƙarin malamai tare da ba su karin girma bisa cancanta. Hakan yana daga cikin babban burin mu na inganta matakan koyarwa da kuma ƙarfafa gwiwar malamai domin su ci gaba da bayar da gudunmawar su,” inji shi.
Daraktan ya yaba wa malaman bisa haƙuri, jajircewa da sadaukarwar da suke nunawa wajen koyarwa da tarbiyyar al’umma, tare da tabbatar musu cewa Niger-SUBEB za ta ci gaba da tallafa musu wajen bunƙasa ƙwarewar su da cigaban rayuwar su ta aiki.
Ya shawarci malaman da su ɗauki karin girman a matsayin wata hanya ta nuna godiya ga irin gudunmawar da suka bayar a baya, tare da ɗaukar sabon nauyin da ke gaban su na ƙara inganta harkar ilimi.
A nasu ɓangaren, malaman LGEA na Suleja da Tafa sun nuna godiyarsu ga hukumar bisa kokarin da take yi, inda suka ce aikin tantancewar ya ƙara musu ƙwarin gwiwa da amincewa da tsarin karin girman.
Hukumar ta ce shirin na daga cikin matakan da take ɗauka domin inganta ƙwarewa da nagarta a tsakanin malaman makarantu, tare da tabbatar da cewa sun samu damar ci gaba da samar da ingantaccen ilimi da zai dace da muradun Jihar Neja da Nijeriya baki ɗaya.
Lokogoma ya bayyana cewa da zarar an kammala aikin tantancewar, za a gaggauta aiwatar da karin girman, domin malaman da suka cancanta su fara cin moriyar sabon matsayin su da Gwamnatin Jihar Neja ta amince da shi.






