Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce zuba jarin da Gwamnatin Tarayya take yi a manyan makarantu ta hannun Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFund) zai taimaka wajen samar da damar bunƙasa noma, ma’adanai, makamashi da sauran fannonin tattalin arziki a yankin Arewa ta Tsakiya.
Idris ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Lokoja, Jihar Kogi, yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na TETFund na shiyyar Arewa ta Tsakiya na shekarar 2026.
Ministan ya ce dole ne jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi da ke yankin su kasance masu alaƙa da buƙatun cigaban yankin, tare da samar da ɗaliban da suka kammala karatu masu ƙwarewar da ta dace da fannonin noma, haƙar ma’adanai, masana’antu, fasaha da sauran fannoni.
Ya ce: “Saboda haka, dole ne jami’o’in mu, kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi su kasance masu alaƙa da waɗannan damarmaki, tare da samar da masana kimiyya, injiniyoyi, ƙwararrun harkokin noma, masana fasaha da ’yan kasuwa da ake buƙata domin amfani da ɗimbin damar da Arewa ta Tsakiya take da ita.”
Ya ce an nuna ƙudirin Gwamnatin Tarayya a cikin tallafin TETFund na shekarar 2026, inda aka ware kusan ₦2.53 biliyan ga kowace jami’ar gwamnati, ₦1.87 biliyan ga kowace kwalejin kimiyya da fasaha, da kuma ₦2.06 biliyan ga kowace kwalejin ilimi.
“Waɗannan ba alƙaluman kasafi kawai ba ne. Suna wakiltar ɗakunan gwaje-gwaje da za a iya samar da kayan aiki a cikin su, ɗakunan lacca da za a iya ginawa, ɗakunan karatu da za a iya ingantawa, bincike da za a iya tallafawa, da ɗalibai da za su iya karatu a ingantattun wurare,” inji shi.
Ministan ya jaddada buƙatar ƙarfafa alaƙa tsakanin manyan makarantu da masana’antu, yana mai cewa bai kamata cibiyoyin ilimi su mayar da hankali kawai kan samar da waɗanda suka kammala karatu ba, ya kamata su kuma mai da hankali kan bincike, ƙirƙire-ƙirƙire da samar da ayyukan yi.
Ya bayyana muhimmiyar rawar da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), ilimin fasaha da na sana’o’i, koyar da dabarun zamani da shirye-shiryen koyar da sana’o’in dogaro da kai ke takawa wajen faɗaɗa damarmaki ga matasan Nijeriya.
Ya ce: “Don haka, ilimi ba kawai zuba jari ba ne a tattalin arziki; zuba jari ne a tsaron ƙasa da zaman lafiyar al’umma.”
Idris ya buƙaci TETFund da ta ci gaba da tabbatar da gaskiya, sa ido da riƙon amana wajen amfani da kuɗaɗen tallafin, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa shawarwarin da aka bayar a taron sun haifar da matakan da za a iya auna sakamakon su.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya ce dole ne manyan makarantu su wuce samar da waɗanda suka kammala karatu kawai, su koma cibiyoyin bincike da samar da hanyoyin warware matsalolin ƙasa a aikace.
Ya ce: “Muna buƙatar binciken da zai magance matsaloli a noma, haƙar ma’adanai, kiwon lafiya, masana’antu, Ƙirƙirarrar Basira (AI), makamashi mai sabuntawa, da tsaro. Dole binciken mu ya samar da hanyoyin magance matsalolin da za su inganta rayuwar jama’ar mu.”
Ya ƙara da cewa ya kamata manyan makarantu su taimaka wajen mayar da albarkatun ƙasa da ƙwarewar jama’ar yankin zuwa samar da isasshen abinci, bunƙasar masana’antu, samar da ayyukan yi da cigaba mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda Farfesa Babatunde Bernard ya wakilta; tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Kyaftin Idris Wada; Shugaban Kwamitin Amintattu na TETFund, Rt. Hon. Aminu Bello Masari; da sauran manyan baƙi.






