• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 4, 2026
in Ilimi
A A
0
Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki
Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, yana miƙa makullin ɗaya daga cikin motocin ga Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami'ar Abdulƙadir Kure, Minna (AKUM, Farfesa Mohammed Kuta Yahaya, yau a Abuja

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, yana miƙa makullin ɗaya daga cikin motocin ga Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami'ar Abdulƙadir Kure, Minna (AKUM, Farfesa Mohammed Kuta Yahaya, yau a Abuja

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, yana miƙa makullin ɗaya daga cikin motocin ga Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Abdulƙadir Kure, Minna (AKUM, Farfesa Mohammed Kuta Yahaya, yau a Abuja

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, ya raba motocin aiki ga jami’an gudanarwar Jami’ar Abdulƙadir Kure, Minna (AKUM) domin inganta gudanar da ayyukan su da sauƙaƙa zirga-zirgar su.

Da yake jawabi yayin bikin miƙa motocin a Abuja, gwamnan ya bayyana cewa samar da motocin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin sa na ƙarfafa harkokin ilimi da samar da ingantaccen yanayin aiki ga shugabannin cibiyoyin ilimi.

Ya ce motocin za su taimaka wajen sauƙaƙa ayyukan jami’an gudanarwar jami’ar tare da ƙara masu ƙwarin gwiwar gudanar da nauyin da aka ɗora masu yadda ya kamata.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa tana ci gaba da ba fannin ilimi fifiko, yana mai cewa jin daɗin malamai da sauran ma’aikatan jami’o’i yana daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin sa ta mayar da hankali a kai.

Ya taya jami’an gudanarwar jami’ar murnar samun motocin, tare da ƙarfafa masu gwiwar su ci gaba da yin aiki tuƙuru domin ɗaga darajar jami’ar.

Haka kuma ya yi nuni da muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin ilimi, musamman ganin akwai Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai da sabuwar Jami’ar Noma da Sauyin Yanayi ta Abdulsalami Abubakar da aka amince da kafawa a Mokwa.

Jerin motocin da aka raba

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Abdulƙadir Kure, Farfesa Mohammed Kuta Yahaya, ya yaba wa Gwamna Bago bisa wannan tallafi, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen bunƙasa ilimi.

Ya ce tallafin da gwamnan ke bai wa jami’ar ya taimaka wajen ƙara yawan masu neman gurbin karatu a makarantar, tare da inganta martabar ta a idon jama’a.

Yahaya ya ƙara da cewa a yanzu Jami’ar Abdulƙadir Kure tana daga cikin jami’o’in jihohi da suka fi jan hankalin ɗalibai a Nijeriya.

Ya bayyana cewa burin Gwamna Bago na faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi na ci gaba da zama gaskiya, yana mai cewa gudunmawar da gwamnan yake bayarwa wajen bunƙasa jarin ɗan’adam abin koyi ne ga sauran masu ruwa da tsaki.

A taron ba da motocin
Tags: Farfesa Mohammed Kuta YahayaGwamna Mohammed Umaru BagoJami'ar Abdulƙadir KureMinna (AKUM)motoci
Previous Post

CBN ya ɗauki matakan daƙile kaka-gidan kamfanonin fintech, tare da kare haƙƙoƙin masu harkokin kuɗi

Next Post

Tinubu ya amince da ƙarin albashi har kashi 80 ga jami’an sojoji

Related Posts

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja
Ilimi

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

August 29, 2026
Ilimi

Niger-SUBEB ta tabbatar da ƙarin girma ga malaman da suka cancanta

August 22, 2026
Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris
Ilimi

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

August 20, 2026
Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya
Ilimi

Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ƙulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki a jami’o’i
Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

July 14, 2026
Jami’ar Capital City ta naɗa Sarkin Kano Sanusi II a matsayin Uban Jami’a
Ilimi

Jami’ar Capital City ta naɗa Sarkin Kano Sanusi II a matsayin Uban Jami’a

June 20, 2026
Next Post
Tinubu ya amince da faɗaɗa rundunar sojin ƙasa zuwa rukunoni 12 tare da ɗaukar sababbin sojoji 28,000

Tinubu ya amince da ƙarin albashi har kashi 80 ga jami’an sojoji

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!