• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
May 12, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
CBN

CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin kashe kuɗi da kula da harkokin kuɗi daga gwamnatocin jihohi, domin tabbatar da nasarar sauya tsarin manufofin kuɗi zuwa tsarin da zai yi tasirin kan daƙile hauhawar farashi.

Da yake jawabi yayin wani taro a sakatariyar Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, wato Nigeria Governors’ Forum (NGF) da ke Abuja, Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da Manufofin Tattalin Arziki, Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa sauya tsarin zuwa tsarin dakushe hauhawar farashi, yana nufin komawa ga tsarin da ya fi dogaro da ƙa’idoji, gaskiya da hangen nesa, wanda ke buƙatar cikakken haɗin kai tsakanin Babban Bankin bankin Ƙasa da Gwamnatocin Jihohi.

 

A cewar wata sanarwa da CBN ya fitar ƙarshen makon jiya, Dakta Abdullahi ya ce duk da cewa CBN ne ke da alhakin gudanar da manufofin kuɗi domin shawo kan hauhawar farashi, matakan kashe kuɗi da manufofin kasafin kuɗi na jihohi suna taka muhimmiyar rawa wajen tasirin hauhawar farashi a ƙasa mai tsarin tarayya kamar Najeriya.

 

Ya bayyana cewa tsarin kashe kaifin hauhawar farashi yana da alaƙa sosai da sarrafa yadda jama’a da masu kasuwa ke sa ran tattalin arziki zai kasance.

 

Yana kuma mai gargaɗin cewa rashin daidaito ko yawan kashe kuɗi ba tare da tsari ba daga gwamnatocin jihohi na iya ƙarfafa ko raunana manufofin kuɗin da CBN ke aiwatarwa.

 

Ya ce jihohi suna tasiri ga hauhawar farashi ta hanyoyi da dama, ciki har da:

Shawarwarin karɓar bashi, taruwar bashin cikin gida, salon kashe kuɗi, albashin ma’aikata,

gudanar da ayyukan gine-gine da ci gaba, da sauran su.

 

Sai kuma tsarin da gwamnatocin jihohi ke bi wajen biyan ‘yan kwangila ta hanyar bashi da kuma rashin daidaito wajen sarrafa kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke rarraba wa jihohin (FAAC), da irin yanayin yadda jihohin ke biyan bashi, duk abubuwan yin la’akari da su ne.

 

“Ya ce a ƙasa kamar Nijeriya inda ake ta ƙoƙarin daƙile hauhawar farashi, to a gaskiya yanayin da gwamnatocin jihohi ke kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, zai iya gurgunta wannan ƙoƙarin na kashe kaifin hauhawar farashi.” Inji shi.

 

Ya buƙaci jihohi su rage dogaro da cin bashin wucin-gadi, su tabbatar da cewa bashin da suke karɓa ya dace da ƙarfin biyan bashin su, sannan su inganta sahihancin kasafin kuɗi da kyakkyawan hasashen kuɗaɗen shiga.

Daga nan ya shawarce su cewa su riƙa fifita muhimman fannoni wajen kashe kuɗi, su riƙa daidaita tsarin kasafin kuɗi da yanayin tattalin arziki.

Abdullahi ya bayyana manyan ayyuka huɗu da suka rataya a wuyan gwamnatocin jihohi, waɗanda ya lissafa kamar haka: Kiyaye tsari da daidaito a harkokin kashe kuɗi.

Karɓar bashi cikin hikima da bin tsarin matsakaicin lokacin biyan kuɗi. Inganta haɗin kai wajen sarrafa kuɗi da bashi. Sai kuma ƙarfafa tara kuɗaɗen shiga na cikin gida.

Ya yi gargaɗin cewa kashe kuɗi ba tare da tsari ba, yawan ƙarin kasafin kuɗi da tara bashin alaƙaƙai, duk suna iya haifar da matsalar yawan kuɗi a kasuwa tare da ƙara haɗarin hauhawar farashi.

Ya ƙara da cewa shirin kashe kaifin hauhawar farashi wani yunƙuri ne na ƙasa baki ɗaya, domin samar da daidaito, amincewa da ci gaba mai ɗorewa. Duk da cewa CBN ne ke da alhakin tabbatar da daidaiton farashi, nasarar tsarin tana dogara ne kan yadda dukkan matakan gwamnati za su nuna ɗa’a a harkokin kuɗi.

Ya ce ta hanyar ƙarfafa haɗin kai da sanya daidaiton farashi a matsayin manufa ta bai ɗaya, gwamnatocin jihohi za su taimaka wajen kafa tubalin ci gaban tattalin arziki, samar da ayyukan yi da inganta walwalar jama’a.

Tun da farko, Daraktan Sashen Manufofin Kuɗi na CBN, Victor Oboh, ya bayyana tsarin a matsayin tsarin da ke amfanar iyalai, kamfanoni da gwamnatoci ta hanyar tabbatar da daidaiton hasashen hauhawar farashi, ƙarfafa amincewa da manufofin gwamnati da rage rashin tabbas a tattalin arziki.

Ya jaddada cewa ba za a iya samun daidaiton farashi ta hanyar manufofin kuɗi kaɗai ba, musamman a tsarin tarayya, yana mai cewa kashe kuɗi, karɓar bashi da yadda jihohi ke tafiyar da kuɗaɗen su suna da tasiri kai tsaye kan yawan kuɗi a kasuwa da hauhawar farashi.

A cewar sa, an shirya wannan taro ne domin ƙara fahimtar juna, bunƙasa tattaunawa da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin CBN da gwamnatocin jihohi kan rawar da kowanne ɓangare zai taka domin samun nasarar tsarin.

Tags: bashiCBNjihohi
Previous Post

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

Next Post

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

Related Posts

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa

May 3, 2026
Next Post
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!