Kwana biyar kacal bayan sace ɗalibai mata 24 a makarantar su a Jihar Kebbi, wasu ’yan ta’addan sun kai hari da sanyin safiyar yau Juma’a a Makarantar Firamare da Sakandaren Katolika ta St Mary’s, Papiri, Jihar Neja, inda suka sace ƙananan yara, ɗalibai da malamai tare da barin ɗan sanda mai gadi cikin munanan raunuka.
Harin, wanda ya fara kusan ƙarfe 1:00 na safe, ya ci gaba har zuwa ƙarfe 3:00 na safe lokacin da ’yan ta’addan, ɗauke da makamai, suka bar makarantar tare da waɗanda suka sace.
Zuwa yanzu ba a san yawan waɗanda aka sace ba, amma ana zargin sun kai 57.
Sakataren Yanki na Cocin Katolika na Kontagora, Fada Jatau Luka Joseph, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya la’anci wannan abu da ya auku, yana mai fatan Allah ya dawo da su cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma, Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da sacewar. Kakakin hukumar, SP W.A. Abiodun, ya bayyana cewa a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na safe, rahoto ya nuna cewa wasu ’yan bindiga sun mamaye Makarantar Sakandare ta St Mary’s Private (Katolika), Papiri, Ƙaramar Hukumar Agwara, suka kuma sace adadin ɗalibai da ba a tabbatar da su ba daga ɗakin kwanan su.
Abiodun, wanda ya ce an tura tawagar jami’an musamman domin aikin ceto, ya bayyana cewa: “Za a binciki wannan lamari kuma a ɗauki matakin da ya dace kan shugabancin makarantar saboda ci gaba da gudanar da karatu, saɓanin umurnin gwamnatin jiha na rufe makarantun yankin saboda matsalolin tsaro.”
Ga sanarwar rundunar ’yan sandan:
RUNDUNONIN TAKAITATTUN JAMI’AN ’YAN SANDA, DAKARUN SOJOJI SUN ISA PAPIRI DON CETON GAGGAWA NA ƊALIBAN DA AKA SACE A MAKA RANTAR SAKANDARE TA ST. MARY’S PRIVATE (KATOLIKA), PAPIRI, AGWARA LGA
Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da cewa a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na safe, rahoto ya nuna cewa wasu ’yan bindiga sun mamaye Makarantar Sakandare ta St Mary’s Private (Catholic), Papiri, Agwara LGA, suka kuma sace adadin ɗalibai da har yanzu ba a tantance su ba daga ɗakin kwanan makarantar.
Duk da haka, rundunonin ’yan sanda na musamman, dakarun sojoji da sauran jami’an tsaro suna cikin aikin tantance da kuma neman waɗanda aka sace a cikin dazuzzukan yankin domin ganin an dawo da su cikin lafiya.
Saboda haka, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, CP Adamu Abdullahi Elleman, ya jaddada ƙudirin rundunar na ganin an ceto ɗaliban ba tare da wata illa ba, tare da roƙon jama’a su kwantar da hankalin su, su kuma bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin aikin ceto.
Ya kuma tabbatar da cewa za a gudanar da bincike, kuma za a ɗauki matakin da ya dace kan gudanarwar makarantar saboda ci gaba da gudanar da karatu, saɓanin umurnin gwamnatin jiha na rufe makarantun yankin saboda matsalolin tsaro.
SP W.A. Abiodun
PPRO
Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Neja







