• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

UNGA: Nijeriya ta jaddada ‘yancin kafuwar Falasɗinu

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 25, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
UNGA: Nijeriya ta jaddada ‘yancin kafuwar Falasɗinu
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yana jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York

Nijeriya ta bayyana cewa, mafita ta samar da ƙasashe biyu ita ce hanya mafi kyau da za ta kawo dauwamammen zaman lafiya ga al’ummar Falasɗinu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakin sa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.

Tinubu ya ce: “Ba mu yarda da ganin rayuwar ɗan’adam ta makale cikin jayayya marar ƙarewa ba. Shi ya sa muke tsayawa ba tare da shakka ba, muna cewa mafita ta samar da ƙasashe biyu masu yancin kan su ita ce hanya mafi kyau ga zaman lafiya a Falasɗinu.”

Ya ƙara da cewa da daɗewa al’ummar Falasɗinu suna fuskantar rikice-rikicen da suka jawo zubar da jini da tashin hankali.

“Ba mu zo a matsayin masu ɓangaranci ba, mun zo ne a matsayin masu burin kawo maslaha. Mun zo a matsayin ‘yan’uwa a duniyar da bai kamata ta rage darajar rayuwa ta mutum ɗaya zuwa wani abin wasa a siyasa ba.”

Shugaban ya bayyana cewa mutanen Falasdinu ba “ƙurar rikici” ba ce, su ma ‘yan Adam ne kamar kowa da kowa, masu daraja da ‘yancin rayuwa irin wanda sauran mutane ke morewa.

Ya jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan ƙimar zaman lafiya da haɗin kai a maimakon tashin hankali, ramuwar gayya da zubar da jini.

Tinubu ya ce, Nijeriya za ta ci gaba da yin aiki ta hanyar dandalin haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa don ƙarfafa doka da samar da amincewa tsakanin ɓangarorin dake hamayya.

Dangane da al’amuran cikin gida kuma, shugaban ya ce Nijeriya ta ɗauki matakai masu wahala don sake fasalin tattalin arziki da kawar da tallafin man fetur da kuma tsarin canjin kuɗi, domin a samu ci gaba da bunƙasar tattalin arzikin da zai kawo zaman lafiya mai ɗorewa.

Tags: FalasɗinuKashim ShettimaMajalisar Ɗinkin DuniyaUNGA
Previous Post

Cika shekara 65: Tinubu ya taya tsohon minista Gwarzo murna

Next Post

Jami’an KAROTA sun kama kayan sola da kwamfutoci na naira miliyan 80 da ɓarayi suka sace a Kano

Related Posts

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Ƙasashen Duniya

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

April 17, 2026
Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta
Ƙasashen Duniya

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

April 3, 2026
Next Post
Jami’an KAROTA sun kama kayan sola da kwamfutoci na naira miliyan 80 da ɓarayi suka sace a Kano

Jami'an KAROTA sun kama kayan sola da kwamfutoci na naira miliyan 80 da ɓarayi suka sace a Kano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!