Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon Darakta-Janar na Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA) bayan ya tsige Malam Salihu Abdulhamid Dembos daga muƙamin.
Wanda aka naɗa ɗin shi ne Mista Rotimi Pedro.
Naɗin ya biyo bayan raɗe-raɗin da aka sha yi a cikin ‘yan kwanakin nan cewa an cire Dembos daga shugabancin hukumar gidajen talbijin ɗin ta ƙasa.
A cikin wata sanarwa da Segun Imohiosen, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya rattaba wa hannu, gwamnati ta kuma bayyana wasu naɗe-naɗen na daraktoci uku mata a hukumar.
Sababbin naɗe-naɗen da inda suka fito dai su ne:
- Darakta-Janar: Rotimi Pedro (daga Kudu-maso-yamma)
- Babbar Daraktar Kasuwanci: Karimah Bello (daga Arewa-maso-yamma)
- Babbar Daraktar Labarai: Stella Din Jacob (daga Arewa-ta-Tsakiya)
- Manajar Daraktar kamfanin NTA Enterprises Limited: Sophia Essahmed (daga Arewa-ta-Gabas)
Shugaba Tinubu ya buƙaci sababbin waɗanda aka naɗa ɗin da su yi aiki tare don sake inganta da haɓaka NTA ta hanyar kawo sababbin dabaru da za su ƙarfafa ayyukan da hukumar ke yi waɗanda kuma suka dace da aikin jarida na zamani.
Shi dai Salihu Abdulhamid Dembos da aka tsige, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa shugaban NTA Oktoba 2023, kuma Tinubu ya ƙara naɗa shi bayan an ci zaɓe.
Shi kuma Pedro da aka naɗa, ɗan Legas ne kuma masani kan sha’anin wasanni da nishaɗantarwa wanda ya daɗe a harkar aikin talbijin.
An bayyana cewa sababbin manyan daraktocin da aka naɗa ɗin za su maye gurbin waɗanda Tinubu ya naɗa a cikin Satumba 2024.






