• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe babban kwamandan ISWAP a Arewa-maso-gabas

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 31, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe babban kwamandan ISWAP a Arewa-maso-gabas
Sojojin Nijeriya a bakin daga

Sojojin Nijeriya a bakin daga

Sojojin “Operation Haɗin Kai” sun sake samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ’yan ta’adda a Arewa-maso-gabas, inda suka kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP mai suna Julaibib a yankin Kimba, cikin Ƙaramar Hukumar Damboa ta Jihar Borno.

Bayanai sun nuna cewa marigayin na daga cikin manyan jagororin da ke ta’addanci a yankin Gujba na Timbuktu Triangle, kuma kashe shi ya jefa ’yan ISWAP cikin ruɗani tare da raunana tsarin jagoranci da umarnin su.

A wasu hare-hare na daban, sojojin tare da haɗin gwiwar “Civilian Joint Task Force” sun kashe ’yan ta’adda uku a wani kwanton ɓauna tsakanin Ngazalgana da Lamusheri a Borno, inda suka ƙwato bindigogin ƙirar AK-47 guda biyu.

Haka kuma, a Tsokorok da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza, sojoji sun fatattaki ’yan Boko Haram/ISWAP, suka kashe guda ɗaya tare da ƙwato babura biyu, ba tare da asara a ɓangaren sojoji ba.

A Jihar Adamawa kuwa, sojoji sun daƙile yunƙurin fashi da makami a Mubi ta Arewa, inda suka kama mutum biyu da ake zargi, sannan suka ƙwato makamai da kayayyaki.

A wani sintiri kuma, sojoji tare da ’yan sa-kai sun fafata da ’yan ta’adda a yankin Amtasa–Washim, suka ceto wata mata da aka sace tare da ƙwato bindigogi da harsasai.

Rundunar “Operation Haɗin Kai” ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-gabas.

Tags: OperationHaɗinKaisojoji
Previous Post

Shettima ya halarci ɗaurin aurarraki a Kaduna

Next Post

Sun tsara kashe ni, inji Ministan Tsaro kan yunƙurin juyin mulki

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Sun tsara kashe ni, inji Ministan Tsaro kan yunƙurin juyin mulki

Sun tsara kashe ni, inji Ministan Tsaro kan yunƙurin juyin mulki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!